Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da fara kidayar yawan jama’a da gidaje na shekarar 2023 a ranar 3 ga watan Mayu.
Dakta Garba Abari, mamba ne a kwamitin yada labarai da bayar da shawarwari kan kidayar jama’a da gidaje ta kasa na shekarar 2023, ya tabbatar da hakan a ranar Lahadi a Abuja yayin tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN).
Ya ce, za a gudanar da kidayar ne acikin kwanaki uku, za a fara a ranar 3 ga watan Mayu zuwa 5 ga watan Mayu a fadin kasar.
Abari, wanda shi ne Darakta-Janar na Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA), ya bayyana cewa, aikin kidayar ba zai tsallake kowa ba, zai kidaya kowane mutum da gida akan tsari na kasa.
A cewarsa, an sauya ranar da aka fara tanada ne sabida dage zaben gwamnoni da na majalisun jihohi da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi a shekarar 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp