Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya misalta matakin shari’a da jam’iyyar PDP reshen jihar da dan takararta na gwamnan Jihar Jibrin Barde suka dauka kan takararsa a babban zaben 2023 a matsayin Soki-burutsu.
Gwamnan ta bakin daraktan yada labarai na Gwamnatin jihar, Ismaila Uba Misilli, ya shaida ma wakilinmu cewa sa’ayin masu zuwa kotun ba zai karkatar da hankulansa da na Gwamnatinsa daga shimfida kyawawan ayyukan kyautata cigaban al’ummar jihar ba.
Da ya ke maida martani kan shari’ar da PDP da dan takararta suka shigar a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja inda suke neman kotun ta haramta wa gwamnan da mataimakinsa damar shiga zaben 2023 bisa zargin wai sun gabatar da takardun bogi wa hukumar zabe mai zaman kanta, gwamnan ya ce, “Duk da cewa har yanzu ba a kawo mana takardar sammacin kotun ba. Don haka sai an kawo mana sammacin za mu fitar da cikakken bayani kan karar.”
Hadimin gwamnan ya kara da cewa, “Amma a bisa abubuwan da kafafen yaɗa labarai suka fitar, dukkanin batutuwan nasu cike yake da son zuciya da kuma zarge-zargen mara tushe balle makama da jam’iyyar da dan takararta suka yi bisa fargabar shan kasa a zaben 2023 da za su iya fuskanta.”
“Kamata ya yi su fuskanci masu zabe da manufofinsu ba wai su zago ta bayan gida da zarge-zargen marasa kan-gado ba,” ya shaida.
Ya daura da cewa, “INEC da sashin shari’a a yanzu ba su katsalandan. Muna nan muna zaman jiran sammacin kotun domin mu maida amsa yadda ya kamata.”