Gwamnatin Jihar Kebbi ta kaddamar da kwamitin mutane 18 domin shiryawa tare da lura kan fara tura Maniyyata zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2024.
Hukumar Alhazai ta kasa, NAHCON, ta ware filin jirgin kasa da kasa na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi a karon farko, domin fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya wanda aka shirya gudanarwa a ranar 15 ga watan Mayu, 2024.
- Mutane 17 Sun Shiga Hannu Kan Hada-hadar Canjin Kudi Ba Bisa Ka’ida Ba A Kano
- Tinubu Ya Dawo Nijeriya Bayan Shafe Mako Guda A Turai
Da yake gabatar da bikin kaddamar da kwamitin a sansanin Alhazai na Dakta Nasir Idris da ke Birnin Kebbi, Shugaban Kwamitin, Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Yakubu Bala Tafidan Yauri, ya gode wa Gwamnan Jihar da ya ba su damar yi wa kasa hidima.
Mamba a kwamitin, kuma dan Majalisa mai wakiltar Danko-Wasagu ta Gabas a majalisar dokokin jihar, Muhammad Garba Bena, Wanda ya wakilci sakataren gwamnatin, ya bukaci dukkan mambobin da su jajirce wajen ganin an samu nasarar kaddamar da jirgin Alhazan Nijeriya na farko a jihar Kebbi.
“Gwamnatin tarayya ta mayar da Jihar Kebbi a matsayin wani babban dandali na aikin Hajjin bana, dole ne mu hada karfi da karfe don yin aiki tukuru wajen ganin mun tabbatar da amincewar da hukumomin tarayya suka yi mana.” Inji shi.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi, Alhaji Faruq Aliyu Yaro Enabo, ya gode wa Gwamna Nasir Idris bisa yadda ya bai wa kwamitin tallafi da kuma kayan aiki don samun nasarar gudanar da jigilar Maniyyatan daga filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello International Airport da ke Birnin Kebbi.