A shekarar 2024, an kammala jigilar fasinjojin da yawansu ya kai biliyan 1.46 a filayen jiragen sama na kasar Sin yayin da yawan tashi da saukar jiragen sama ya wuce miliyan 12.4, adadin sun karu da kashi 15.9 bisa dari da kuma kashi 5.9 bisa dari, idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara. Hakan ya nuna cewa, duka alkaluma masu alaka da harkokin sufuri sun kafa tarihi.
Kazalika, a ranar 21 ga wata, kungiyar filayen jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin, da kwalejin nazarin kimiyya da fasahar jiragen sama masu daukar fasinja ta kasar Sin, da sauransu sun fitar da “Rahoton kimanta ingancin hidimar filin jirgin sama na shekarar 2024”, inda rahoton ya ce, akwai daidaito da ci gaba a zirga-zirgar jiragen sama na yau da kullum a kasar Sin. A shekarar ta 2024, yawan zirga-zirgar jiragen sama na yau da kullum a kasar ya kasance kashi 87.1 cikin dari, wanda ya kai sama da kaso 80 cikin dari tsawon shekaru bakwai a jere. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp