ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, July 12, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akpabio Da Abbas Sun Yi Gargaɗi Kan Ciwo Bashi Ba Tare Da Sa Ido

by Rabi'u Ali Indabawa
10 months ago
Akpabio

Majalisar Wakilai Ta Ƙasa (NASS) ta yi gargaɗin cewa idan ba a yi taka tsantsan ba, matsayinta na bashin gwamnati, wanda ya kai Naira tiriliyan 149.39  daidai da Dala biliyan (97) a kwata na farko na shekarar 2025, na iya haifar da haɗari ga makomar ƙasa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ne suka yi wannan gargaɗin a taron shekara-shekara na 11 a babban taro na Ƙungiyar Kwamitocin Binciken Asusun Jama’a ta Yammacin Afirka (West Africa Association of Public Accounts Committees – WAAPAC) da aka gudanar a Abuja jiya.

  • Akpabio Ya Ƙaryata Jita-jitar Ba Shi Da Lafiya
  • Kotu Ta Yi Watsi Da Buƙatun Akpabio Kan Dakatar Da Sanata Natasha

Taron shekara-shekara an shirya shi ne ta Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati na Majalisar Wakilai, mai taken: “Ƙarfafa Kula da Majalisa kan Bashin Gwamnati.”

ADVERTISEMENT

Akpabio, wanda Sanata Osita Izunaso, shugaban Kwamitin Kasuwar Hannayen Jari na Majalisar Dattawa ya wakilta, ya bayyana cewa rashin kulawa da bashin gwamnati na iya sanya makomar ‘yan ƙasa cikin haɗari kuma ya raunana dimokuradiyya a faɗin yammacin Afirka.

Ya bayyana cewa kulawar majalisa ba za ta yi watsi da lamarin wajen tabbatar da daidaiton kuɗaɗen gwamnati ba, kuma idan aka sarrafa bashin yadda ya kamata, zai zama muhimmin aiki wajen ɗaukar nauyin ayyukan more rayuwa, da ci gaban ɗorewa.

LABARAI MASU NASABA

2027: INEC Ta Tsawaita Wa’adin Miƙa Sunayen ’Yan Takara

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

Akpabio ya yi kira ga duk ƙasashen membobin WAAPAC da su samar da izinin majalisa ga kwamitocin da suka dace, yana mai cewa hakan zai tabbatar da ‘yancinsu da ingancinsu wajen kare dukiyar jama’a.

“Bashin gwamnati, idan aka sarrafa shi yadda ya kamata, zai zama aiki ne mai muhimmanci wajen ɗaukar nauyin ci gaba, ayyukan more rayuwa, da ci gaba mai ɗorewa. Amma idan aka bar shi ba tare da sanya ido ba aka ɓoye shi cikin rashin gaskiya, zai zama nauyi da ke sanya makomar ‘yan ƙasa cikin haɗari.

Wannan shi ya sa majalisa ba za yi watsi da sanya ido a kansa wajen bashi kulawa ba.

“Kwarewar Nijeriya ta nuna cewa idan kwamitocin majalisa suka samu ikon doka, gaskiya da riƙon amana sun ƙaru, kuɗi ya yi ƙarfi, to dimokuraɗiyya ta ƙara inganci,” in ji shi.

A nasa ɓangaren, Abbas ya gargaɗi cewa basussukan Nijeriya sun kai wani matsayi mai hatsari, inda ya buƙaci majalisun dokoki a faɗin Yammacin Afirka su ƙarfafa sa ido kan aro na gwamnati domin kare makomar ‘yan ƙasashensu.

Da yake magana a madadinsa, Jagoran Majalisar Wakilai, Hon. Julius Ihonɓbhere, Abbas ya bayyana cewa jimillar basussukan gwamnatin Nijeriya ya kai Naira tiriliyan 149.39 (kimanin Dalar Amurka biliyan 97) a zangon farko na shekarar 2025, wanda ya nuna ƙaruwar ta yi tsanani daga Naira tiriliyan 121.7 a shekarar da ta gabata.

Ya bayyana damuwa kan matsayin bashin da aka kwatanta da GDP, wanda a halin yanzu ya kai kusan kashi 52 cikin 100, sama da iyakar kashi 40 cikin 100 da doka ta ƙayyade.

Ya ce: “Wannan karya haddin bashi ne luma hakan wata alama ce ta matsin lamba ga ɗorewar tattalin arziki. Hakan ya nuna gaggawar buƙatar ƙarfafa sa ido, yin aro cikin gaskiya da bayyana dukkan bayanai, da kuma samun haɗin kai domin tabbatar da cewa kowace Naira da aka aro ta samar da ainihin amfanin tattalin arziki da zamantakewa.

“A duk faɗin Afirka, matakin bashi ya kai wani mummunan matsayi. A shekarar 2022, jimillar bashin ƙasashen nahiyar ya kai Dala tiriliyan 1.8, inda bashin wajen shi kaɗai ake sa ran zai zarce Dala tiriliyan 1 a shekarar 2023.”

Ya ce: “Ƙasashe da dama yanzu suna cikin mummunan yanayi na cin bashin da aka kwatanta da GDP: misali; Sudan na da kaso 344, Angola kaso 136.8, Ghana 84, Kenya kusan 70, yayin da Afirka ta Kudu ta haura kaso 77.”

Kakakin majalisar ya lura cewa a faɗin Afirka, bashi ya zama matsalar tsarin tattalin arziki, inda ƙasashe da dama ke kashe kuɗi fiye da na kula da lafiya da sauran muhimman ayyuka wajen biyan bashin da suka karɓa.

A cewarsa, kashi 35 na bashin na ƙasashen Turai ne na masu ba da rance masu zaman kansu, kashi 39 na ƙungiyoyin haɗin gwiwa irin su IMF da Bankin Duniya, kashi 13 kuma na ƙasashen da ke bayar da rance kai tsaye (bilateral creditors), sannan kashi 12 daga Ƙasar China.

Abbas ya ce Nijeriya ta ƙuduri aniyar jagorantar kafa tsarin duba bashin ƙasashen Yammacin Afirka ta majalisar dokoki ƙarƙashin WAAPAC, domin daidaita rahotannin bashi, samar da ƙa’idojin yanki kan gaskiya da bayyana bayanai, tare da bai wa majalisu damar samun bayanai cikin lokaci don inganta bincike.

Akpabio
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Mun Ɗauki Nauyin Karatun Masu Digiri Ta Hanyar Sayar Da Ƙosai Da Ƙuli-ƙuli —Wasu Ƴan Kasuwa
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilanta Na Sake Fasalin Hukumar NYSC

MASU ALAKA

inec
Manyan Labarai

2027: INEC Ta Tsawaita Wa’adin Miƙa Sunayen ’Yan Takara

July 12, 2026
Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta
Manyan Labarai

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Manyan Labarai

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

July 11, 2026
Next Post
Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya

Gwamna Lawal Ya Tallafa Wa Ƙananan ’Yan Kasuwa Da Sama Da Naira Biliyan Ɗaya

LABARAI MASU NASABA

NiMet Ta Gargaɗi Jihohi 27 Kan Barazanar Ambaliyar Ruwa A Farkon Watan Yuli

NiMet Ta Gargaɗi Jihohi 27 Kan Barazanar Ambaliyar Ruwa A Farkon Watan Yuli

July 12, 2026
2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Amince Da Jamilu Gwamna A Matsayin Gwamnan Gombe

2027: Masu Ruwa Da Tsaki Sun Amince Da Jamilu Gwamna A Matsayin Gwamnan Gombe

July 12, 2026
NDLEA Ta Gargaɗi Masu Sana’ar Keke NAPEP Kan Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi

NDLEA Ta Gargaɗi Masu Sana’ar Keke NAPEP Kan Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi

July 12, 2026
inec

2027: INEC Ta Tsawaita Wa’adin Miƙa Sunayen ’Yan Takara

July 12, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Tallafa Wa Yara Masu Buƙatu Na Musamman Shi Ne Burina

July 12, 2026
Annalena Baerbock: Kasar Sin Babbar Mai Goyon Bayan Tsarin Mabambantan Bangarori Ce

Annalena Baerbock: Kasar Sin Babbar Mai Goyon Bayan Tsarin Mabambantan Bangarori Ce

July 11, 2026
Sin Ta Kalubalanci A Tabbatar Da Tsagaita Bude Wuta A Gabas Ta Tsakiya

Sin Ta Kalubalanci A Tabbatar Da Tsagaita Bude Wuta A Gabas Ta Tsakiya

July 11, 2026
Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027

Amurka Ta Yi Alƙawarin Sa Ido Sosai A Zaɓen Nijeriya Na 2027

July 11, 2026
Babban Jami’i: Nazartar Mahangar Xi Jinping Mabudi Ne Na Fahimtar Kasar Sin Ta Zamani

Babban Jami’i: Nazartar Mahangar Xi Jinping Mabudi Ne Na Fahimtar Kasar Sin Ta Zamani

July 11, 2026
Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

Sautin Muryar Da Aka Fallasa Kan El-Rufai Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

July 11, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.