Sarkin kudan Alhaji Muhammad Bello Haladu ya Taya Mai Martaba sarkin Zazzau Kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Kaduna, Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli CFR murnar shiga Sabuwar Shekarar 2024.
A sakon nasa Sarkin kudan Muhammad Bello Haladu ya Taya gwamnan jihar Kaduna Sanata Uba sani murnar shiga Sabuwar Shekarar Miladiyya, tare da Fatan samun nasara Da Kuma Dauki daga Allah madaukakin sarki.
- Kyakkyawar Dabi’ar Gawuna Ke Kara Wa Kanawa Aminta Da Nagartarsa -Ibrahim Mabo
- ‘Yan Gudun Hijira Sun Koka Da Tsadar Gidan Haya Da Abinci A Kudancin Kaduna
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da wakilin yada labaran Masarautar Kudan, Yusuf Ibrahim Kudan ya fitar a ranar Lahadi, 31 ga watan Disamba, 2023.
Sarki Haladu Har ilayau ya Kuma Yaba da Irin salon jagorancin Mai Martaba sarki Gami da jajircewarsa, wanda ya samo asali da Irin kwarewa da yake da ita na tafiyar da Masarautar Zazzau Zuwa ga Babban Matsayi.
Sarkin ya kuma jinjinawa Hakimin kudan, Tukuran Zazzau, Alhaji Halliru Mamuda da Kuma na Hunkuyi, Mayanan Arewan Zazzau, Alhaji Muhammad Aminu Ashiru saboda kokarinsu da jajircewarsu na ganin yankunan nasu sun samu ci Gaba.
Daga bisani sarkin ya Kuma ja hankalin Al’ummar yankin dasu hada kai da juna domin Ciyar da yankin Gaba.
A cewarsa “Babu wata cigaba da Za a iya samu ba tare da nuna kauna, Hadin Kai da zaman lafiya da juna ba”.