ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, June 4, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Kyakkyawar Dabi’ar Gawuna Ke Kara Wa Kanawa Aminta Da Nagartarsa -Ibrahim Mabo

by Abdullahi Muh'd Sheka
2 years ago
Mabo

ALHAJI IBRAHIM MU’AZZAMU MABO, Shugaban Kungiyar ‘GAWUNA HAS COME’ na Jihar Kano, gogaggen dan kasuwa, mai fashin baki a kan harkokin ci gaban Jihar Kano da harkokin kasuwanci, sannan makusanci ga Dakta Nasiru Yusif Gawuna, wanda kotun sararon kararrakin zabe da ta daukaka kara suka ayyana a matsayin halastaccen Gwamnan Jihar Kano, ya wakilinmu na Kano; ABDULLAHI MUHAMMAD SHEKA, kan dalilan kafa kungiyar ‘Gawuna Has Come’, da sauran abubuwan da kungiyar ke hasashe kan makomar Kano a nan gaba kadan. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance:

Da farko, da wa muke tare?

Alhamdulillahi! Muna kara godiya ga Allah. Sunana Alhaji Ibrahim Mu’azzamu Mabo Sani Mainagge, an haife ni a Unguwar Sani Mainagge, na yi karatun firamare a Sani Mainaggen; daga nan na wuce zuwa GATC Gwale, sai kuma Makarantar Hadaka ta Gwamantin Tarayya da ke Karaye.

ADVERTISEMENT

Daga nan kuma na sake wucewa Makarantar Share Fagen Shiga Jami’a ta Kano (CAS), kazalika, na halarci Makarantar Nazarin Harkokin Shari’a ta Aminu Kano ‘School for Legal studies’,  inda na karantar harkokin shari’a, daga  nan ne kuma sai na tsallaka zuwa Jami’ar Al-Lahada da ke Kasar Nijar, inda na yi sa’ar samun digirina na farko a kan harkokin shari’a. Bayan nan ne kuma, sai na tsunduma harkokin kasuwanci, wanda kuma yanzu haka ni ne Shugaban Kungiyar ‘Gawuna Has Come’ na Jihar Kano.

Duba da yanayin tarihinka, yaya aka yi ka tsinci kanka a harkokin siyasa?

LABARAI MASU NASABA

Har Yanzu Ana Yin Allah-wadai Da Cin Amanar Da Aka Yi Wa Kwankwaso – Hon. MB Aliyu

Dalilin Da Ya Sa PDP Ke Cikin Rikici, Za Ta Dawo Da Karfin Ta —Saraki

Masha Allah, kamar yadda ka sani ne akwai dalilai da dama wadanda ke sa mutum tsunduma cikin harkokin siyasa. Amma magana ta gaskiya, ni tun tasowata ina da ra’ayin tallafa wa jama’a,  domin kuwa tun shekara 13 da suka gabata na kirkiri wata gidauniya, wadda na sanya wa suna Gidauniya IMY (IMY  FOUNDATION), wadda na fara tallafa wa marayu da masu karamin karfi a karkashinta, ta hanyar kula da harkokin rayuwa da kuma karatunsu.

Ko ka taba samun kanka a wasu kungiyoyi na dalibai, wadanda suka haska maka shiga wannan gwagwarmaya ta siyasa?

Ko shakka babu, an samu kai a cikin ire-iren wadannan kungiyoyi, domin kuwa an dan taba su gwargwadon iko, wannan tasa ganin yadda muka mu’amalanci marayu da masu karamin karfi, ya ba mu damar kallon yadda za mu samu damar fadada irin wannan mu’amala, wadda hakan tasa muka ga dacewar tsunduma wadannan harkoki na siyasa.

Ko masu karatu za su iya jin dalilin kafa kungiyar ‘Gawuna Has Come’?

Kasancewar Siyasar Kano na da alaka da tarbiya da addininmu, wannan tasa muka kafa wannan kungiya, wadda muka mayar da hankali a kan batun addu’o’i, wadda ko shakka babu ita ce takobin duk wani mai fatan samun ingantacciyar nasara. Sannan, mun fara da gudanar da addu’o’i a kan siyasara Dakta Nasiru Yusif Gawuna,  kamar yadda aka sani tarbiyyarsa ta nuna yadda ya fi bukatar addu’a, bayan yin dogon nazari a kan haka; sai muka ga dacewar tattaro mutanen da muka aminta da shahadarsu a kan tafiyar Gawunan, wadanda muke da tabbacin za su ba mu gudunmawar addu’o’i, don haka gaskiyar magana da haka muka fara.

Har ila yau, ganin yadda kotu ta ayyana Dakta Nasiru Yusif Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Kano, sannan tunda wadancan ba su hakura da hukucin kotun farko ba, ya sa muka mai da hankali tare da rada wa wannan kungiya suna na ‘Gawuna Has Come’, domin ci gaba da yin luguden addu’o’i, domin dorewar wannan nasara.

Shin kai ne ka rada mata wannan suna ta kai ga nada ka a matsayin shugabanta?

Magana ta gaskiya ba ni ne na rada mata wannan suna ba, kasnacewar a kwai mutane masu kima da hangen nesa ya sa aka samar da wannan suna, sannan kuma ba ni ne na nada kaina a matsayin shugaban wannan kungiya ba, ganin cancantata ya sa aka aminta da na rike shugabancinta a matsayin rikon kwarya.

Haka zalika,  idan ka dubi harkokina ka san zai yi wuya a ce na kuma hada da wannan shugabanci, amma saboda karfin tafiyar ya sa na ajiye dukkanin wasu abubuwa nawa a gefe guda na mayar da hankali a kan wannan lamari na harkokin addu’a gwargwadon iko, sannan kuma Alhamdulillahi; muna ganin nasara kwarai da gaske.

Mene ne ya bai wa Mabo sha’awar hada tafiya Dakta Gawuna?

Sanina da Gawuna ba na yanzu ba ne, domin kuwa na san shi tun lokacin da ya fara zama a unguwarmu ta Dandago, sannan kamar yadda ka sani ne tsakanin Dandago da Sani Mainagge tazarar babu yawa, har ila yau na san yadda ya zauna da iyayenmu lafiya ga kuma kyakkyawar tarbiyya da girmama na gaba, wannan tasa nake da yakinin cewa matukar Allah ya rabauta Kano da shi, ko shakka babu za ta hau saiti dodar ba tare da wata lankwasa ba.

Me ya sa kake ganin shi ya fi dacewa da samun wannan dama?

Ai wannan duk wani mai kyakkyawan tunani ya san Gauwna shi ne mafi dacewa da mulkin Kano a daidai irin wannan lokaci, musamman ganin yadda wadancan mutanen suka haifa wa jihar matsaloli, musamman a bangaren yadda suka hargitsa nutsuwar wasu daga cikin ‘yan kasuwa ta hanyar rushe musu guraren neman halaliyarsu.

Wannan ne ya sa muke da yakinin cewa, idan Allah ya mika wulayar Jihar Kano da Kanawa a gare shi, ko shakka babu za a yi matukar farin cikin gaske, wannan tasa muka tashi tsaye domin ci gaba da yin luguden addu’o’i, sakamakon muna da yakinin yana daga cikin sunnar Alllah addu’ar wanda aka zalunta karbabbiya ce. Don haka, wannan kyakkyawar manufa ta wannan kungiya ce ta sa dumbin mutane masu daraja da kima ke yin tururuwa wajen shigowa cikinta, wanda hakan ya ke baiwa kowa mamaki.

Ko batun rusau da aka yi wa ‘yan kasuwa na cikin dalilan da suka sa Mabo zabar shiga wannan shiri na gudanar da addu’o’i?

Kwarai kuwa, ai wannan ko kadan ba abun mamaki ba ne idan hakan ya sa ni shiga, domin kowa ya san yadda Kano ta shahara ta fuskan kasuwanci, sai kuma ga gwamnati ta zo da wani tsari na kassara harkokin kasuwancin da ‘yan kasuwa. Don haka, kenan ka ga ya zama wajibi mu fito mu yi addu’a tare da fatan Allah ya fatattaki wadannan mutane ya kuma kawo mana wadanda za su taimaki ‘yan kasuwa da harkokinsu na kasuwancin baki-daya.

Wace irin gudunmawa Alarammomi ke bai wa wannan kungiya, musamman ta fuskar addu’o’in da kuka sanya gaba?

Alhamdulillahi, muna kara yi wa Allah godiya, muna kuma kara gode wa wadannan Alarammomi da Mahaddata Alkur’ani, domin kuwa zuwa yanzu, mun samar da wasu rundunonin Alarammomi guda biyar-biyar a kowace karammar hukuma cikin Kananan Hukumomin Jihar Kano 44, wadanda a kullum muke tare da su, muke kuma ci gaba gaba yin addu’o’i na musamman a irin wannan lokaci da muke dakon hukuncin karshe daga kotun koli ta tarayya, wanda muka kwashe kwanaki 40 muna luguden addu’o’i da saukar alkur’ani mai girma, domin fatan Allah ya tabbatar da mana da nasarar Dakta Nasiryu Yusif Gawuna da Mataimakinsa Alhaji Murtala Sule Garo.

Shin ko akwai wani kalubale da ka fuskanta tun bayan kafa wannan tsari na yin addu’o’i?

Babu sahakka akwai wannan kalubale, domin wasu ma gani suke yi kamar mun yi kutse ne don biyan bukatar kanmu,  wanda kuma gaskiya ba haka lamarin yake ba, mu Kanon ce a gabanmu muka ita muke kallo da makomarta, sakamakon yakinin da muke da shi na cewa, idan Allah ya kawo Gawuna; ko shakka babu Kano za ta dauki irin saitin da ya kamata.

Haka zalika, kalubalen daga ko’ina akwai shi; cikin gida da waje kuma babu abin da ke gabana da ya wuce isowar Dakta Nasiru Yusuf Gawuna, sannan ba na kallon duk wata hamayarsu; domin kuwa ba ta gabana, abin da ma nake kallo shi ne kamar so ake yi a kawar da hankalinmu daga harkar addu’o’in baki-daya, sakamakon irin nasarorin da ake samu.

Mene fatanka na karshe da za ka isra wa masu karatu?

Babban fatan da muke yi shi ne, Allah ya tabbatar wa da Dakata Nasiru Yusuf Gawuna da Mataimakinsa Murtala Suke Garo wannan nasara, sannan ina kara kira ga jama’armu; musamman Alarammomi da Mahaddata Alkur’ani cewa, su kara himma wajen ci gaba da yin wadannan addu’o’i, domin yanzu Gawuna ya fi bukatar addu’a, sannan bayan Allah ya tabbatar da shi a matsayin Gwamnanmu, mu sake kara addu’ar Allah ya kuma yi riko da hannunsa.

Mabo
Abdullahi Muh'd Sheka
+ postsBio
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    Sakamakon Matsin Lambar Jami’an Tsaro, ‘Yan Ta’adda Na Fuskantar Ƙarancin Abinci
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    Kisan Gillar Mutum 7 A Kano: Sarakuna Da Malamai Da Iyaye Sun Nemi A Gaggauta Yanke Wa Waɗanda Ake Zargi Hukunci
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    MACBAN Ta Nemi Amurka Ta Cire Sunanta Daga Jerin Waɗanda Ta Ƙaƙabawa Takunkumi
  • Abdullahi Muh'd Sheka
    https://hausa.leadership.ng/author/abdullahi-muhd-sheka/
    Faɗace-Faɗacen Daba Da Ƙwacen Waya A Kano Ya Ɗauki Sabon Salo

MASU ALAKA

Har Yanzu Ana Yin Allah-wadai Da Cin Amanar Da Aka Yi Wa Kwankwaso – Hon. MB Aliyu
Tattaunawa

Har Yanzu Ana Yin Allah-wadai Da Cin Amanar Da Aka Yi Wa Kwankwaso – Hon. MB Aliyu

April 10, 2026
 Saraki Zai Jagoranci Kwamitin Gyara Jam’iyyar PDP 
Tattaunawa

Dalilin Da Ya Sa PDP Ke Cikin Rikici, Za Ta Dawo Da Karfin Ta —Saraki

April 4, 2026
Zan Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Bunkasa Yanki Na —Sarkin Tilden Fulani
Tattaunawa

Zan Hada Hannu Da Gwamnati Wajen Bunkasa Yanki Na —Sarkin Tilden Fulani

March 28, 2026
Next Post
Ana Ci Gaba Da Alhinin Rasuwar Ghali Na’Aabba

Ana Ci Gaba Da Alhinin Rasuwar Ghali Na’Aabba

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Ofishin NAGGW Zuwa Kano Domin Yaƙi Da Hamada

June 4, 2026
Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

Mambobin NYSC 4, Soja da Mutum 1 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Adamawa

June 4, 2026
Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

Sarki Sanusi II Ya Tuɓe Rawanin Mai Unguwar Rikadawa Kan Badaƙalar Fili

June 4, 2026
Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

Tawagar Masanan Dakile Yaduwar Cututtuka Ta Sin Ta Isa DR Congo

June 3, 2026
Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

June 3, 2026
Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

Han Zheng Zai Halarci Taron SPIEF Karo Na 29 A Rasha Tare Da Gudanar Da Ziyarar Aiki A Belarus

June 3, 2026
Majalisa Ta Nemi Tinubu Ya Canza Dabarun Yaƙi Da Ta’addanci Don Kawo Ƙarshen Kashe-kashe

’Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Fice Daga APC Zuwa ADC da PRP

June 3, 2026
An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

An Fara Watsa Shirye-Shirye Masu Taken “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” Da Sauran Fina-Finan Bayyana Labaran Sin A Kasar Laos

June 3, 2026
Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

Tambuwal Ya Jajanta Wa Waɗanda Harin ’Yan Bindiga Ya Shafa A Sokoto, Ya Nemi A Ƙara Tsaro

June 3, 2026
Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

Gwamnatin Beijing Ta Amince Da Kafa Cibiyar Kirkire-Kirkiren Fasahar Lissafi Mai Nasaba Da Sararin Samaniya

June 3, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.