Kwamitin zartarwa na shiyyar Kudu maso Yamma na jam’iyyar APC, ya shirya tsaf don gudanar da yakin neman tazarcen shugaban kasa Bola Tinubu a karo na biyu a 2027.
Shugabannin sun kuma bayyana shirye-shiryen daukar masu taya su kira ga zabar Tinubu a kowace Unguwa gabanin babban zaben 2027.
- Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027
- Rangwame: Tinubu Ya Bada Umarnin Sake Bitar Tsarin Yadda Ake Karɓar Haraji
Jim kadan bayan kammala taron da suka gudanar a Akure, babban birnin jihar Ondo a ranar Laraba, jiga-jigan jam’iyyar APC, sun ce manufar taron kuma, tabbatar da cewa duk shirye-shiryen shugaban kasa da tsare-tsare na tattalin arziki da nufin rage tsadar rayuwa sun kai zuwa ga talakawa.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron kwamitin, Shugaban Jam’iyyar APC na shiyyar Kudu maso Yamma, Hon. Isaac Kekemeke, ya ce, “Burinmu shi ne, yankin Kudu-maso-Yamma dole ne ya yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yakin neman zabe kamar yadda yankin Arewa maso Yamma ya saba yi wa marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp