Wata sabuwar kungiyar fitattun jagororin siyasa daga yankin krewa ta fito, mai suna ‘League of Northern Democrats’ (LND), wadda ta ce za ta gudanar da wani babban taro mai ma’ana don farfado da martabar siyasa da tattalin arzikin yankin arewacin Nijeriya.
Kungiyar wadda ta bayyana aniyarta na hada kai tare da mayar da yankin arewa a matsayin sahun gaba a fagen siyasar Nijeriya, ta kuma bayyana cewa gaba daya damuwarta ita ce ci gaban arewacin Nijeriya, inda ta jaddada cewa ba ta gabatar da wani bukatu na kashin kai ga kowa sai ga yankin arewacin Nijeriya.
- Na Yi Alƙawarin Kawo Wa APC Kano A Zaɓen 2027 – Doguwa
- Jawabin Tinubu Kan Kisan Sarkin Gatawa Ya Bar Baya Da Ƙura
Kungiyar mai mutane 226, karkashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, a matsayin shugaban riko da Umar Ardo, a matsayin mai kira da Hon. Emmanuel Jime a matsayin sakataren rikon kwarya da tsofaffin gwamnoni da ‘yan majalisar tarayya da ‘yan kasuwa.
Bayan Shekarau da Ardo, wasu daga cikin manyan masu fada a ji a kungiyar sun hada da Alhaji Tanko Yakasai, Sanata. Ibrahim Ida, PhD, CON (Wazirin Katsina); Kabir Tafida (Sarki Fadan Sakkwata); Falalu Bello; Dakta Jamilu Isyaka Gwamna (Sardauna Gombe); Emmanuel Jime da kuma Mohammed Kumalia.
Sauran sun hada da Malam Salihu Lukman, Amb. Usman Sarki, Injiniya Dallaji Nuhu, Farfesa Usman Yusuf, Muktari Abubakar Tafawa Balewa, Aminu Shehu Shagari, da Murtala Shehu Yar’adua (Tafidan Katsina), da sauransu.
Bayan gudanar da wani taro da aka yi a cibiyar ‘Yar’adua da ke Abuja, kungiyar ta yanke shawarar ba da fifiko kan hadin kan siyasar arewacin Nijeriya.
“Bayan cimma matsaya a tsakaninmu, mun himmatu wajen inganta al’ummarmu da samar da hadin kai. Wannan hadin kai ne zai zama ginshikin kokarin da muke yi na mayar da arewa a matsayin jagaba a fagen siyasar Nijeriya.”
Sun kuma yanke shawarar rubuta wa masu ruwa da tsaki a arewacin Nijeriya don samun goyon bayansu da shiga harkokin kungiyar.
A cikin wadanda za a tuntuba sun hada da dukkan tsoffin shugabannin kasa da dukkan tsoffin mataimakan shugaban kasa da masu rike da madafun iko da tsofaffin shugabannin majalisar dattawa da tsofaffin shugabannin majalisar wakilai da tsoffin alkalai da tsoffin hafsoshin soja da sufeto Janar na ’yansanda da Kwanturolan Janar na Kwastam da shugaban hukumar shige da fice da na hukumar jidan yari da manyan-manyan dattawan jihohi da ‘yan kasuwa da manyan ma’aikata da kungiyoyin kwadago da sauran wasu abubuwan da suka dace.
A cewar kungiyar, shigar wadannan masu ruwa da tsaki na da matukar muhimmanci wajen samun nasarar ayyukanta.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan taron, Malam Shekarau ya ce kungiyar za ta mayar da hankali ne kan batutuwan da suka shafi ci gaba arewacin Nijeriya ba muradin kowa ba.
Ya ce ‘yan kungiyar za su bullo da wasu dabaru na yadda za a inganta al’umma a yankin arewa ta hanyar wayar da kan jama’a kan irin kalubalen da suke fuskanta da bukatunsu na yau da kullum.
Ya ce za su wayar da kan al’umma kan bukatar shugabanci na gari, bunkasar tattalin arziki da samun dukiya da dacewa da ilimi da tsaro da hadin kai.
Ya kara da cewa, “Tunani ne na siyasa, ba wai game da wani mutum ko jam’iyya ba, kuma yana da matukar muhimmanci game da zaben 2027. Wannan batun da ya dauki shekaru mai yawa. Muna son samar da kundi wanda ya zarce shekara guda, shekara biyu, ko shekara 10.”
A nasa bangaren, Umar Ardo ya ce, “Mutanen arewa za su hada kai wuri guda domin magance matsalolin yanki arewa. Ba mu damu da matsalar nada mukamai ba, mun damu da matsalolin rashin tsaro, yunwa, talauci da na tattalin arziki da ke addabar arewa.
“Ba mu damu da batun nade-naden ba, domin yana zuwa ne wuce, amma muhimmin batu shi ne a warware wadannan matsaloli da suke damun arewa.”