Kwanan baya, firaministan kasar Fiji Sitiveni Rabuka ya kai ziyarar aiki na tsawon kwanaki 10 a kasar Sin. Kuma a yayin ziyararsa a Sin, wakilin Babban Gidan Rediyo da Talabijin na Kasar Sin wato CMG ya yi masa intabiyu.
A shekarar 1994, Mista Rabuka ya taba kai ziyara a kasar Sin, yanzu shekaru 30 sun riga suka wuce, a wannan karo, ya fara ziyararsa daga gundumar Malipo dake lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar.
- Kasar Sin Ta Kara Ware Kudaden Agajin Gaggawa Ga Lardin Liaoning Dake Arewa Maso Gabashin Kasar
- Sin Na Kira Da A Gudanar Da Tsarin Sa Ido Mai Inganci Mai Zaman Kan Sa Ga Batun Zubar Da Dagwalon Ruwan Fukushima
Gundumar Malipo ta taba kasancewa wuri mafi fama da talauci a kasar Sin, amma ta cimma nasarar kawar da talauci a shekarar 2020, sakamakon jerin manufofin da aka aiwatar, gami da matakan raya sana’o’i da aka dauka.
A wannan karo, Mista Rabuka ya kai ziyarar aiki a wasu kauyukan dake gundumar, inda ya kara fahimtar manufar farfado da kauyuka ta kasar Sin, da ma yadda ake gudanar da harkar noma da aikin kare al’adun gargajiya a wurin, har ya je gidajen mazauna kauyukan domin jin labaransu. Dangane da wannan batu, Mista Rabuka ya yi bayani cewa, “akwai abubuwa da dama da kasarmu za ta koyo, bayan na isa wurin, na rubuta bayanin da suka yi min, kuma na yi ta tunani, ta yaya za mu iya mai da ayyukan da aka yi a kauyukan, su zama manyan ayyukan da za mu iya yi don raya larduna da ma kasa baki daya.” (Mai Fassara: Maryam Yang)