Gabanin zaɓen 2027, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi zaɓe bisa ga ra’yin gashin kansu ba duba ga ƙabila ko yanki ba.
|Atiku, jigo ne a jam’iyyar ADC, ya bayyana kabilanci a matsayin abin da ke kawo cikas ga ci gaban kasa kuma muguwar cuta ce wacce dole ne kowa ya bar ta, musamman masu ƙaramin ƙarfi.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Kola Johnson, ya fitar, Atiku ya ce, manyan ‘yan siyasar ne ke rura wutar ƙabilanci da yanki don raba kan al’umma maimaikon kallon kansu a matsayin ‘yan ƙasa ɗaya da ba za a iya raba su ba.
A cewar Atiku, wannan kalmomi (ƙabilanci da yanki) an tanade su ne don raba kan jama’a da nufin cimma burinsu na siyasa ta hanyar roƙon ’yan ƙabilarsu da kada su zaɓi wani ɗan takara wanda ya fito daga wata ƙabila’ maimakon tantance shi da kyawawan halayensa.