Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya tabbatar da cewa, a shirye yake domin ya yi aiki tare da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023 Mr. Peter Obi domin ceto ƙasar nan daga halin ni’yasu da take ciki a halin yanzu.
Peter Obi wanda ya zo jihar Bauchi a ranar Alhamis domin ziyartar Bala Mohammed don ganin sun tattauna da yin tuntuɓa a tsakaninsu domin ganin an nemi hanyoyin da za a cire ƙasar nan daga matsalolin da suke akwai.
- Tabbaci Kan Bunkasuwar Tattalin Arziki Mai Dorewa A SinTabbaci Kan Bunkasuwar Tattalin Arziki Mai Dorewa A Sin
- ECOWAS Ta Kaddamar da Dakarun Yaƙi da Ta’addanci
A jawabinsa, tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter ya ce, akwai buƙatar dukkanin ‘yan siyasan Nijeriya su haɗa kansu waje guda domin ceto ƙasar nan.
Ya ce, muddin ‘yan siyasan Nijeriya ba su haɗa kansu waje guda ba, ƙalubalen da suke cikin ƙasar nan za su yi wuyar kawuwa. Ya ce, akwai kuma buƙatar tunƙarar matsalolin taɓarɓarewar tattalin arziki a Nijeriya.
Ya ce, tuntuɓar da suka fara da gwamnan Bauchi a matsayinsa na fitaccen ɗan siyasa a Arewa kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP ya yi ne ba wai don son zuciyarsu ba, illa sai don son da suke yi da cigaban ƙasar nan da nemi mafita.
Ya lura kan cewa akwai buƙatar a fara magance matsalolin talauci a Nijeriya kafin a tunƙari sauran matsaloli. Ya yi fatan cewa za su ci gaba da irin wannan tattaunawar domin nema wa Nijeriya mafita.
Shi kuma a jawabinsa, gwamna Bala Muhammad ya ce, tabbas akwai buƙatar ‘yan siyasa su ajiye ra’ayoyinsu su nemi yadda za su haɗa kai waje guda domin ceto Nijeriya da tabbatar da shugabanci na kwarai, sai ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da Peter Obi.
Bala wanda ya misalta Peter Obi a matsayin jagoran ‘yan adawa a Nijeriya, “Ko ma dai menene za a ce, a shirye nake na yi aiki tare da Peter Obi, mun jingine wane wane wane wane domin nemi shugabanci na kwarai a ƙasar nan.”
Bala Mohammed ya ce lokaci ya yi da za a ajiye banbance-banbance a tunƙari haƙiƙanin zahiri tare da kawar da matsalolin da suke damun Nijeriya. Ya kuma ce, ba magana ce ake ta jam’iyya ba, illa sai don ƙasar baki daya.
Daga cikin tawagar Peter Obi akwai tsohuwar ministan kuɗi, Mrs. Nenadi Usman wadanda suka ziyarci Sarkin Bauchi Rilwanu Sulaiman Adamu bayan da suka ziyarci gwamnan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp