Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Olabode George ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta iya tsayar da dan arewa takarar shugaban kasa na zaben 2027 ba.
Ya ce, “A gaskiya ban fahimci maganganun da ake yi na cewa dan Arewa ne zai sake yin takarar shugaban kasa a 2027 karkashin jam’iyyarmu ba.
- Da Ɗumi-Ɗumi: Jam’iyyar APC Ta Kori Shugabanta Na Jihar Bauchi, Aliyu Misau
- Yanzu-yanzu: Gwamna Diri Na PDP Ya Lashe Zaben Bayelsa
“Dan Arewa ba zai iya zama dan takarar shugaban kasa a jam’iyyarmu a 2027 ba, wannan shi ne gaskiyar magana. Tun da farko wasu ‘ya’yan jam’iyyarmu da ke ingiza wannan ajanda sun san babu adalci a lamarin.
“Ba ni adawa da ‘yan Arewa. Domin kuwa, babban abokina dan Arewa ne, amma ‘yan PDP su fahimci wannan gaskiyar tun kafin lokaci ya kure. Dan PDP daga kudancin kasar nan ya zama dan takararmu kuma mu mara masa baya domin ya kayar da dan takarar APC a zaben 2027.
“Har zuwa 2031, babu wanda ya isa ya yi tunanin tsayawa shugaban kasa na jam’iyyarmu daga Arewa. Ya kamata dattawan jam’iyyarmu na gaskiya su tashi su fadi gaskiya.
“Gaskiya tana da daci amma dole ne a fadi ba tare da wani tsoro ba. Iyayen da suka kafa jam’iyyarmu wasu ma sun bai duniya, amma ba za mu taba iya mantawa da su ba,” in ji shi.
George ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zanta da manema labarai a Legas, ya gargadin ‘ya’yan jam’iyyar PDP cewa jam’iyyar ba za ta ci gaba da wanzuwa ba har sai idan ta koma kan tafarkin maganata.
Ya ce ya bayyana hakan ne saboda jam’iyyar tana cikin wani mawuyacin hali, idan har ba a gaggauta magance matsalolin jam’iyyar ba, to za ta samu kanta a cikin mummunan yanayi.
George ya ce lura cewa wasu gwamnonin na adawa da shirin mayar da dan Arewa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a 2027.