Da alamu dai rikicin babbar jam’iyyar adawa ta PDP bai kai ga kawo karshe ba, yayin da takaddamar ta kara kamari a tsakanin kwamitin gudanarwar jam’iyyar ta kasa, inda wasu bangarori masu madafun iko guda biyu suka fitar da sanarwar manema labarai masu cin karo da juna kan wani muhimmin al’amari na jam’iyyar.
Ba da jimawa ba sai ga wani bangare a cikin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar wanda sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba ya wakilta a wani taron manema labarai, inda ya bayyana amincewar jam’iyyar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na korar Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakatarenta na kasa da kuma nada Sunday Kelly Enemchukwu Udeh-Okoye a madadinsa da mataimakin sakataren yada labarai na kasa, Ibrahim Abdullahi, a yayin wani taron manema labarai na daban ya bayyana cewa Sanata Anyanwu ya ci gaba da zama a mukaminsa har sai an yanke hukunci na karshe daga kotun koli.
- Shirin Tallafinmu Ga Nijeriya A 2025 Zai Kai Ga Asalin Mabukata – Wakilin MDD
- Nazarin CGTN: Tsauraran Manufofin Amurka Na Shan Suka
Da yake zargin Ologunagba, Abdullahi ya yi ikirarin cewa ya yi hakan ne bisa ga umarnin mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Umar Damagum domin nada sakataren yada labarai na kasa.
A ranar 24 ga watan Disamba ne kotun daukaka kara da ke Inugu ta kori Anyanwu tare da bayyana Udeh-Okoye a matsayin sahihan sakataren jam’iyyar na kasa biyo bayan karar da aka shigar na neman tsige Sanata Anyanwu daga wannan mukami bayan ya fito takarar a jam’iyyar a watan Nuwamba a zaben Gwamnan Jihar Imo a 2023.
Udeh- Okoye wanda ya kasance tsohon shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa reshen kudu maso gabas ta tsayar a matsayin wanda zai maye gurbin Sanata Anyanwu, ya yi zargin cewa shi Sanata Anyanwu ya rasa mukaminsa na sakataren kasa a lokacin da ya nemi tikitin tsayawa takara tare da samun tikitin PDP a zaben gwamnan Imo.
Sai dai a lokacin da Sanata Anyanwu ya kutsa kai cikin sakatariyar jam’iyyar PDP ta kasa bisa rashin amincewa da hukuncin kotun daukaka kara, ya yi watsi da matsayin Ologunagba kan lamarin a matsayin ra’ayinsa na kashin kansa, inda ya dage cewa ya ci gaba da zama sahihan sakataren jam’iyyar PDP na kasa har sai an yanke hukuncin karshe na shari’ar daga kotun koli.
A halin da ake ciki, yayin da Sanata Anyanwu ya nace cewa, “Na daukaka kara kan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, kuma na shigar da kara a dakatar da aiwatar da hukuncin, har sai an warware wadannan batutuwa, na ci gaba da zama sakataren jam’iyyar na kasa,” Ologunagba, ya ci gaba da cewa Ude-Okoye ya ci gaba da zama sahihin sakataren jam’iyyar PDP na kasa bisa karfin hukuncin kotun daukaka kara.
Masu sharhi kan harkokin siyasa da masu kallon wasan kwaikwayo da ke kunno kai a jam’iyyar PDP na ganin cewa rigimar da ke tsakanin Sanata Anyanwu da Ude Okoye kan batun sakatariyar jam’iyyar na iya kai jam’iyyar ta kara tsunduma cikin rikicin shugabanci. Sun kuma kara da cewa rigingimun na iya haifar da tsangwama ga fitintinu a cikin jam’iyyar wanda zai haifar da rarrabuwar kai a cikin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar, lamarin da zai iya samar da rikici ga wasu gwamnonin jam’iyyar da kuma ‘yan majalisar dokokin kasar da tuni aka yi zargin cewa suna cikin rikicin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Misali, wata majiya mai tushe ta PDP ta bayyana cewa, duk da cewa hadiman Gwamna Sheriff Francis Oborebwori sun musanta batun sauya shekarsa zuwa APC, amma hakika yana matakin karshe na shirin barin PDP.
“Gaskiyar magana ita ce gwamnan ya damu da wa’adinsa na biyu, yana jin cewa jam’iyyar PDP ta shiga wani hali mara kyau, kuma ba ta da hurumin tabbatar masa wa’adi na biyu.,” inji majiyar.
An dai bayyana cewa saboda yunkurin sauya sheka da ya yi a baya-bayan nan, Gwamna Oborebwori ya kasa hakura da sukar jam’iyyar APC da shugabanninta.