Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ce kadai za ta yanke hukunci kan makomarsa a zaben 2027 mai zuwa.
Atiku ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da BBC a ranar Juma’a.
- Shugabannin Bankuna Sun Ci Bashin Naira Biliyan 549 Cikin Shekara 5
- Gwamnonin Arewa-Maso-Yamma Sun Nemi Goyon Bayan MDD Kan Magance Ƙalubalen Yankin
Ya bayyana cewa, lokaci ya yi da za a yanke shawara kan batun tsayawarsa takarar shugaban kasa ko akasin haka a zaben da ke tafe.
Sai dai ya ce ganawar da ya yi da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, na iya zama wata alama ta yin hadaka a babban zaben 2027.
“Na bayyana karara tun a zaben da ya gabata cewa idan ‘ya’yan jam’iyyarmu sun amince da kudu-maso-gabas su fitar da dan takara, duk mun amince,” in ji Atiku.
Atiku ya tabbatar da yiwuwar yin kawance tsakanin jam’iyyun adawa gabanin zaben 2027 duk da cewa bai bayar da cikakken bayani kan hakan ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya karyata rahotannin da ke yawo cewa zai yi ritaya daga siyasa bayan zaben 2023.
“Mun yi yaki sosai har ma da gwamnatocin sojoji; balle gwamnatocin farar hula. Don haka, idan aka yi tunanin akasin haka, to mafarki mutane ke yi. Ba za mu taba ja da baya daga yaki da rashin adalci da rashin shugabanci ba nagari ba. Har yanzu ban gaji da gwagwarmayar siyasa ba,” in ji shi.