Bayani ya nuna cewa, shugabannin da manyan ma’aikatan bankuna kasar sun karbi basukan fiye da Naira Biliyan 549 daga bankunansu a cikin shekara biyar.
Wannan bayanan yana kunshe ne cikin rahoton shekara biyar (daga 2019 zuwa 2023) da bankunan suka mika wa hukumar kula da huldar kudi ta kasa (Nigerian Edchange Limited).
- Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Zanta Da Takwaransa Na Tanzania
- Xi Ya Jaddada Muhimmancin Kyautata Tsarin Yawon Bude Ido Na Zamani
Sai dai kuma bayanin ya nuna cewa, basukan da shugabannin bankunan suka karba ya matukar raguwa a shekarar 2023.
Cibiyoyin kudin da aka yi nazari a kai a shekarar sun hada Access Holdings, Guaranty Trust Holding Company Plc, Zenith Bank Plc, United Bank for Africa, Fidelity Bank, Wema Bank, Stanbic IBTC Holding Plc da kuma FCMB Group.
Raguwar ya samu ne saboda sabuwar dokar da CBN ya fito da shi wanda ya fara aiki a watan 1 ga watan Agusta na shekarar 2023.
Sanarwa wanda wani babban darakta a CBN, Chibuzo Efobi, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa, an soke duk wata doka da ta ci karo da sabuwar doka, kuma an umarci dukkan cibiyoyin kudi su tabbatar da aiwatar da tanade-tanaden da ke tattare da jadawalin dokokin.
A shekarar 2022, basukan da bankuna 10 suka ci a cikin gida ya kai naira biliyan 131.04, bankunan sun hada da Access Holdings, Guaranty Trust Holding Company Plc, Zenith Bank Plc, United Bank for Africa, Fidelity Bank, Wema Bank, Stanbic IBTC Holding Plc, FCMB Group, Unity Bank da kuma Sterling Bank.
Bankin Fidelity ce ke da bashi mafi girma a shekarar sai kuma bankin Unity yayin da bankin UBA ke biye da ita.