Taron kwararru na jam’iyyar PDP (CP-PDP) ya shaida wa Shugaban kasa Bola Tinubu cewa ‘yan Nijeriya ba za su sake zabe shi a 2027 ba, saboda tsananin yunwa da ya jefa al’ummar kasar a ciki.
kungiyar ta PDP ta kuma ce babu wanda zai iya yin magudi a sakamakon zaben shugaban kasa na 2027 da kuma zaben shugabannin kananan hukumomi na Abuja da za a gabatar a watan Fabrairun 2026.
- Sallah: Tinubu Ya Raba Wa ’Yan APC Buhun Shinkafa 7,000 A Zamfara
- Dokar Ta-ɓaci A Ribas: Gwamnonin PDP Sun Ƙalubalanci Hukuncin Tinubu A Kotun Ƙoli
Taron ya bayyana haka ne bayan ganawar da ta gabata a ranar Litinin a matsayin martani ga kalaman Tinubu a lokacin da Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Cif Nyesom Wike ya kai masa gaisuwar Sallah a Abuja.
Shugaban CP-PDP, Barr. Obinna Nwachukwu, ya yi ikirarin cewa APC ba ta da wata dama a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma babban zaben 2027 bisa ga irin mummunan shugabancin da suke gudanarwa a halin yanzu.
“A kowane yanayi, cewa Shugaba Tinubu da magoya bayansa sun damu da zaben shugabannin kananan hukumomi a Abuja da kuma zabukan 2027, a wannan lokaci ya nuna cewa gwamnatin ba ta mayar da hankali kan mulki da ya dace, ya bar al’ummar kasar nan a wargaje ba tare da alkibla, ga tabarbarewar rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki da kuma rashin tabbas a harkokin siyasa tun lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.
“Abin da ke da tabbas shi ne cewa ‘yan Nijeriya ba za su iya yin rufa-rufa ba ta kowace hanya don boye gazawarka da wahalar da suke ciki har su sake jefa maka kuri’unsu a babban birnin tarayya Abuja da kuma zaben 2027,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp