Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), ta gargadi ‘yan siyasa da su daina tura mata kageggen korafe-korafe da ba su da tushe a kan abokan hamayyarsu na siyasa dangane da gabatowar babban zaben 2023.
Shugaban hukumar ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya shaida cewar wasu ‘yan siyasar sun dukufa amfani da hukumar wajen musguna wa abokan hamayyarsu ta hanyar tura korafe-korafe a kansu, ya yi gargadin cewa irin wannan lamarin ba fa zai yi aiki a hukumarsu ba.
- Fasto Ya Dirka Wa ‘Yar Shekara 12 Ciki A Ogun
- Wasu ‘Yan Siyasa Na Daukar Zaben 2023 Na Ko A Mutu, Ko A Yi Rai –INEC
A wata sanarwar da kakakin hukumar, Azuka Ogugua, ya fitar ya nakalto cewa shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya amshi bakwancin shugabannin kungiyar jam’iyyun siyasa (IPAC) a shalkwatar hukumar da ke Abuja.
Ya ke cewa, “kamar al’ada idan lokacin gasa ya zo, tsakanin ‘yan siyasa ana samun hamayya tare da yawan korafe-korafe a kan juna. Wasu za su dukufa wajen ganin sai sun hana ‘wane’ samun dammar yin takara, suna kawo korafe-korafe. Wannan ba shine aikinmu ba, ba za mu shiga cikin irin wannan lamarn ba. Muna kwasan irin wadannan korafe-korafen mu ajiye a gefe.”
Ya ce, suna kokarin wanzar da adalci a tsakanin kowani bangare, don haka ba za su ke amfani da irin wadannan korafe-korafen don musguna ma wani ko wasu ba.
Ya kara da cewa, hukumarsu ta ICPC ta fahimci juna ita da hukumar zabe INEC kan irin muhimman korafe-korafen kan zabe domin yin abubuwan da suka dace.
A nasa jawabin, shugaban IPAC, Injiniya Yabagi Sani, ya ce sun zo ne domin karfafa hadin guiwa da hukumar domin ganin hanyoyin da za su taimaka mata wajen tabbatar da cewa ‘yan siyasan da suke da kashi a duwawunsu ba a zabesu ba.