A wani kokarin da ake na ganin an cike gurbi na kananan yaran da ba a samu yi masu allurar rigakafi ba daga shekara ta 2019 zuwa 2021 gwamnatin tarayya tare da hadin gwiwa na hukumar lafiya ta duniya, sun sake daukar wani sabon tsari na ganin an samu damar yi ma kananan yaran da suka kai milyan 6 da dubu 200,000 rigakafi.
Ana sa ran ko wace shekara za a yi wa yara 930,000 allurar rigakafin.
- Majalisa Ta 10: Zababbun Sanatocin APC Na Arewa Ta Tsakiya Sun Yi Fatali Da Zabin APC
- Yadda Likita Ya Yi Lalata Da Wata Mai Jinya A Asibitinsa A Jihar Kwara
Tawagar hukumar lafiya ta duniya mai kulawa da allurar rigakafin cututtukan da za a iya maganinsu, da kawar da cutar Foliyo da aka fi sani da Shan Inna, Dakta Kofi Boateng, ya bayyana hakan lokacin da aka yi taron samun makama na hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa da wasu Jihohi mai taken hanya mafi dacewa ta tunkarar al’amarin da aka yi a Abuja.
Boateng ya jaddada sanadiyar bullar annobar cutar Kobid 19 akwai yara da suka kamata ayi masu allurar rigakafin da suka kai miliyan 33 da ba samu damar yi masu ba daga shekarar 2019 zuwa 21.
Ya kara bayanin sanadiyar rashin yi ma yaran allurar rigakafin shi ne babban dalilin da yasa Nijeriya take fama da yawan barkewar annobar cututtukan Bakon Dauro, Shawara,da cutar da take kama Makogwaro da ake samun wahalar yin numfashi da sauran wasu cututtuka.
Shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko ta kasa yace manufar taron shi ne na taimakawa Nijeriya cimma manufar sau yara fiye da milyan 6.2 wadanda ba asamu damr yi masu allurar rigakafi daga shekarar 2019. Wannan taro namu da ganin da sai Jihohi sun tabbatar da cewar dukkan sassan kula da lafiyar al’umma sun kara kaimi abinda zai taimaka wajen an samu yiwa adadin yaran da aka yi niyyar yi mawa. Shugaban hukumar lafiya matakin farko ta kasa Dokta Daisal Shuaib ya ce Nijeriya tana son cimma manufar an yi ma yara kashi 80 nan da shekarar ta 2028.
Bugu da kari ya ce cimma muradin kashi 80 kamar yadda aka yi fatar niyyar samu a tsarin da aka yi shekarar 2018 wannan zai kasance ne har zuwa shekara 10, wannan yana nufin ke nan, nan da shekara ta 2028 an samu cimma birin sai dai kuma wani al’amari koma kafin, a kai shekarar 2028 ana iya cimma shi burin. Dangane da tanade-tanaden da aka yi na cimma burin sai Shuaib ya ce, “Muna karin abin da zai taimakawa wajen al’amarin da ya shafi shugabanci amma ba a matakin kasa ba. Muna kara abubuwan da suka zama wajibi, muka san lalle za su taimaka wato kamar ma’aikata kula da lafiyar al’umma da za a iya tura su daga bangaren kasa zuwa Jiha, daga kuma Jiha zuwa mataki na karamar hukuma. Suna yin aiki ne a matsayin tsintsiya madaurinki daya inda al’amarin allurar rigakafi ya taso dole a daure a taimaka.
Wadannan abubuwan su ne muke amfani da su domin cimma buri yayin da kuma ana tabbatar da ana yin al’amuran cikin gaskiya da rikon amana.