Dan wasan gaba na kasar Masar mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Moh Salah, ya nuna rashin jin dadinsa kan rashin zuwan kungiyarsa gasar zakarun turai da za a fafata a badi.
Liverpool ta kasa samun gurbin buga gasar zakarun turai da za a fafata a badi bayan kashin da Chelsea tasha a hannun Manchester United a wasa na 37 na gasar Firimiya, wanda hakan ya sa sai dai Liverpool ta kammala kakar bana a mataki na biyar.
- Kotu Ta Ci Tarar Wadanda Suka Yi Karar Dakatar Da Rantsar Da Tinubu N17m
- Da Dumi-Dumi: Kotun Koli Ta Yi Fatali Da Karar PDP Kan Takarar Tinubu Da Shettima
Dan shekaru 30, Salah ya kara da cewar “ban ji dadin rashin buga gasar zakarun turai a badi ba amma babu komai za mu buga ‘Europa’ kuma za mu nunawa duniya abin da muke iyawa.”