Yara biyu, Ayuba Ishaku mak shekaru 12 da Yakubu Haruna 13, sun samu kuɓuta bayan shafe kusan shekaru shida a hannun ’yan Boko Haram.
An sace su ne a lokacin da suke da shekaru shida da bakwai a ƙauyen Mandaragrau a ƙaramar hukumar Biu ta Jihar Borno a ranar 29 ga Disamban 2019.
- Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9
- EU, Turkiyya Da Sauran Ƙasashe Sun Yi Ta’aziyyar Rasuwar Buhari
A ranar 12 ga watan Yuli, 2025, yaran suka isa ofishin ’yansanda a Maiduguri inda suka bayar da labarin abin da ya faru da su.
Sun ce Boko Haram sun sace su tare da iyayensu, amma daga baya suka yar da iyayen a hanya saboda ƙarfin su ya ƙare.
Sun kai yaran wani sansani a yankin Tumbun Mota da ke Baga, inda suka tilasta musu yin aikin bauta tare da koya musu yadda ake gyara bindiga.
Yaran sun shafe watanni suna shirya yadda za su tsere cikin sirri.
A ranar 10 ga watan Yuli, suka samu dama suka tsere yayin da mafi yawan ’yan Boko Haram suka fita, sauran kuma suna bacci.
Bayan sun yi tafiya a cikin daji na tsawon kwana biyu, suka isa Maiduguri cikin ƙoshin lafiya.
’Yansanda sun tabbatar da cewa yaran suna cikin ƙoshin lafiya a halin yanzu kuma suna samun kulawa.
Hukumomi na ƙoƙarin tuntuɓar iyayensu tare da ba su kulawa don taimaka musu su warke daga raɗaɗin da suka fuskanta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp