Nijeriya ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke ƙoƙarin karɓar gasar tseren motoci ta Formula 1, bayan da ta gabatar da buƙatar karɓar wannan gagarumar gasa a birnin Abuja.
Wannan ci gaba zai sanya Nijeriya ta zama ƙasa ta farko a nahiyar Afrika cikin sama da shekaru 30 da za ta gudanar da gasar tseren Formula 1, wadda ke jawo hankalin miliyoyin masu kallo a faɗin duniya.
- Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja
- Malaman Firamare Sun Janye Yajin Aiki A Abuja, An Umarci Su Koma Bakin Aiki
Shugaban hukumar wasanni ta ƙasa, Mallam Shehu Dikko, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, yana mai cewa wannan mataki yana cikin burin gwamnatin tarayya na ɗaukaka martabar wasanni a ƙasar. Ya bayyana cewa an riga an naɗa Opus Racing Promotions a matsayin wakilai na musamman da za su jagoranci shirye-shiryen gudanar da gasar.
A cewarsa, karɓar baƙuncin gasar Formula 1 ba wai kawai zai bunƙasa wasanni bane, har ma zai buɗe sabbin hanyoyin haɓaka yawon buɗe ido, inganta ababen more rayuwa, da farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa. Ya bayyana cewa ana nazarin dukkan hanyoyin da za su taimaka wajen sauya Abuja zuwa cibiyar duniya ta tseren motoci.
Dikko ya ƙara da cewa wannan shiri yana tafiya kafaɗa da kafaɗa da tsarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na “Sabon Fata” (Renewed Hope), musamman a ɓangaren wasanni da tattalin arziƙi. Tsarin RHINSE yana da nufin janyo hankalin masu zuba jari daga ƙasashen waje da bunƙasa GDP ta hanyar wasanni.
Idan har aka samu nasarar karɓar wannan gasa, za ta buɗe sabon babi a harkar wasanni da kasuwanci a Nijeriya, tare da samar da damammaki ga matasa da masu sana’o’i, da kuma ƙara haskaka ƙasar a idon duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp