Sakamakon kisan gillar da ake zargin wasu sojojin uku da aikatawa ga fitaccen Malamin Addinin Musulunci a Jihar Yobe, Sheikh Muhammad Goni Aisami Gashuwa, a kan hanyarsa daga Kano zuwa Gashuwa da misalin karfe 10:00 na daren ranar Jummu’ar da ta gabata.
Al’amarin da ya daga hankulan al’ummar Nijeriya baki daya tare da kira ga Gwamnatin Tarayya ta biya iyalansa diyya, kuma a gaggauta hukunta sojojin da suka aikata kisan.
Sahihin bayanan da LEADERSHIP Hausa ta samu daga wata majiya a kauyen Chakama, inda aka kashe Sheikh Goni kusa da garin Jaji-maji da ke shalkwatar karamar hukumar Karasuwa sun tabbatar da cewa sojoji uku ne wadanda suke aiki a bataliya ta 241 da ke Nguru a Jihar Yobe, suka yi tarayya wajen kashe Sheikh Goni Aisami, yayin da aka yi nasarar kama biyu wadanda suka hada da Kofura John Gabriel da Kofura Adamu Gideon, sai dai wanda ake zargi na ukun ya gudu.
Majiyar ta kara da cewa, “Akwai alamar hadin baki tsakanin sojan da malamin da ya rage wa hanya da sauran sojoji biyun da suka biyo bayansu, inda suka tare shi kafin ya shiga Jaji-maji, wanda kan kace me dayan da yake cikin mota tare ya soka masa wuka kuma ya tilasta shi tsayawa. Sauran da ke a mota kirar Sharon suka harbe shi.
Baya ga haka sun yi kokarin tafiya da motarsa abin ya gagara lokacin da suka kawar da gawarsa gefen hanya.
“Da safe sun zo da bakanike don ya gyara musu motar, wanda a wannan halin na same su, inda nan take na ankarar da bakanike cewa ko ya lura motar da yake kokarin gyarawa dama-dama take da jini?
“Tun da daren a kauyen muka ji karar tashin bindiga, kuma kafin isowa ta wajen na ga gawar malamin. Nan take ya ankara kuma sai muka hango wata bindiga a jefe a wajen, da suka hankalta mun ganta, shi ne dayan ya zabura ya dauka, sai na kwaceta a hannunsa tare da ba shi umurnin kar ya kuskura ya motsa ko ya sha dalma. A haka muka kama su ni da bakaniken tare da mika su a hannun ‘yansanda da ke garin Jaji-maji.”
Samun labarin an yi wa Sheikh Goni Aisami kisan gilla ya jawo al’ummar garin Gashuwa da Jihar Yobe baki daya sun shiga cikin rudani, wanda hakan yana da nasaba da kyawawan halaye da mu’amalarsa, sannan yanayin kisan da aka yi masa wanda zalunci ne karara. Uwa-uba kuma, Sheikh Goni shahararren mutum ne kuma mai wa’azukan addinin Musulunci, wanda ya kwashe kimanin shekaru 30 yana gudanar da wa’azi, karantarwa da harkokin da suka shafi kawo hadin kan al’umma baki daya.
Bugu da kari, Shehin malamin ya kware wajen gudanar da da’awar da ta fi shafar al’amurran yau da kullum, wanda matasa da ‘yan boko suka fi yawa a tarukan wa’azukansa.
Har ila yau, mutum ne wanda ba ya tsoron bayyana gaskiya komai dacinta ko a gaban waye kuma a kowane lokaci. Sheikh Goni jajirtaccen malami ne wanda yake adawa da nuna bangaranci ko kyama ga wani bangare. Kowane lokaci ya fi karkata ga hadin kai da fahimtar juna tsakanin musulmi ko tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba, kuma an san shi da raha da annashwa tare da barkwanci.
Sheikh Goni yana da dubban matasa a karkashinsa wadanda suke sauraron karatunsa a zauren da yake bayar da karatu. Yana da kima sosai a idon jama’a. An sha artabu da shi dangane da al’amurran da a baya suka jawo raba gari da wasu bangarori, saboda tsayuwarsa kan gaskiya. Wanda hakan ya sanya mayar da wa’azukansa zuwa kofar gidansa bayan sabanin da ya jawo dakatar da shi daga wa’azi a Babban Masallacin Fada. Amma duk da wannan bai hana dubun-dubatar matasa da al’umma tururuwa wajen sauraron tafsirinsa a lokacin watan Ramadan da yake yi a kowace shekara.
Fitar da sunayen sojojin da suka yi wa Sheikh Goni kisan gilla ya harzuka zukatan matasan da ke matukar biyayya ga marigayin, wadanda yanzu haka suna hannun ‘yansanda a Damaturu tare da ci gaba da gudanar da bincike.
Duk da haka, matasan tare da sauran al’umma a Jihar Yobe da Nijeriya baki daya suna ci gaba da kira ga Gwamnatin Tarayya ta biya diyyar jinin Sheikh Goni tare da gaggawa zartas da hukunci ga sojojin da suka aikata kisan.
Bayanai sun nuna cewa Masarautar Bade, Gwamnatin Jihar Yobe da jami’an tsaron farin kaya da ‘yansanda sun taka rawar gani wajen hana tarzoma bayan kisan gillar da aka yi wa malamin.
Matasan sun harzuka matuka, wanda ko shakka babu yi wa malamin adalci ne zai kwantar da hankula ta hanyar biyan iyalansa diyya kuma a hukunta sojojin da ake zargi da kisan gillar, amma sabanin hakan zai iya jawo matasan bayyana fushinsu a zahiri. Sannan duk da yadda gwamnatin Jihar Yobe ta yi amfani da ingantattun matakan gaggawa wajen tausasa zukatan matasan tare da nada kakkarfar tawaga don yi wa iyalai da al’ummar garin Gashuwa ta’aziyyar, ya dace ta ribanya kokarin ta domin dakile duk wata tarzoma.
Baya ga hakan, al’ummar Nijeriya sun nuna alhini tare da kira ga Gwamnatin Tarayya da Jihar Yobe su dauki ingantattun matakan gaggawa wajen hukunta sojojin da suka aikata wannan danyen aikin kuma a biya diyyar, sannan kuma ya kamata gwamnati ta dauki matakin dakile aukuwar hakan nan gaba, saboda yadda hakan ya sha faruwa a garin.
A hannu guda kuma, ita ma kungiyar Izalatul Bidi’a Wa’ikamatu Sunnah ta kasa, ta bukaci a yi wa Shehin malamin adalci tare da biyan iyalansa diyya kuma a hukunta sojojin da suka aikata wannan danyen aikin. A wani bayanin da Shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Bala Lau ya bayyana jiya Litinin.
Haka suma sauran mallamai sun yi makamancin wannan kira kusan a kowane bangaren kasar nan.
A nata bangaren kungiyar ‘Muslim Rights Concern’ (MURIC) ta yi kira da babbar murya ga Gwamnatin Tarayya cewa a gaggauta hukunta sojojin da suka kashe shehin malamin a cikin wata sanarwar da shugaban kungiyar, Farfesa Ishak Akintola, ya sanya wa hannu a ranar Talata a Abuja.
Baya ga kakkarfar tawagar Gwamnan Jihar Yobe ta tura domin yi wa iyalai da al’ummar garin Gashuwa ta’aziyya, Gwamna Mai Mala Buni ya bayar da umurnin daukar mutum biyu daga cikin ‘ya’yan marigayin aikin gwamnati kai-tsaye, domin rage musu dawainiyar rayuwa bayan rasuwar shehin malamin.
Hon. Buni ya bayar da wannan umurnin ne lokacin da wata tawagar ‘yan’uwan marigayin ta ziyarce shi a ofishinsa da ke gidan gwamnatin jihar a Damaturu ranar Talata. Sannan ya ba su kwarin gwiwa da cewa gwamnatinsa za ta binciki al’amarin da ya jawo mutuwar Sheikh Goni tare da ci gaba da tallafa wa iyalansa.
Malam Ibrahim Aisami, wanda ya yi magana a madadin iyalan marigayin ya yaba da karimcin da Gwamna Buni ya nuna musu ta aiko da tawagar don yi musu ta’aziyya tare da tallafa wa iyalan, wanda ya ce zai rage musu radadin wahalhalun da za su fuskanta bayan rasuwar shehin malamin.
A nata bangaren kuma, Shalkwatar Rundunar Sojojin Nijeriya ta Operation Hadin Kai ta 2, da ke yaki da matsalar Boko Haram a Arewa Maso Gabas, ta yi alkawarin hadin gwiwa da ‘yansanda a jihar wajen gudanar da bincike kan kisan gillar da ake zargin jami’anta da aikatawa.
Bayanan hakan yana kunshe a wata sanarwar manema labaru dauke da sa hannun Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Sojojin, Kaftin Kennedy Anyanwu ranar Litinin.
Bugu da kari kuma ya ce, “Shalkwatar Rundunar Sojojin ta 2, ta kafa kwamitin bincike dangane da wannan abin Allah wadai da ya faru, wanda a karshe idan bincike ya tabbatar da hannun wadanda ake zargin, ko shakka babu za su fuskanci hukuncin gidan soja da na sauran al’umma.
“Wannan al’amari ne mara dadin ji kuma abin takaici a ce ya shafi rundunar sojojin Nijeriya da aka sani da hakuri da kuma bin doka da oda bisa ga yanayin aiki.
“Shalkwatar tsaron tana mika ta’aziyya ga iyalai da ‘yan’uwan marigayin da kuma al’ummar Jihar Yobe baki daya, sannan muna jaddada yi muku alkawarin yin adalci kan lamarin.”