Majalisar wakilai ta tarayya, ta tuhumi ma’aikatu da hukumomin gwamnati da badakalar kudade sama da Naira biliyan 103.8, wadanda suka yi daidai da dalar Amurka 950,912.05.
Hakan na faruwa ne, yayin da majalisar ta bukaci hukumar EFCC da ICPC da sauran hukumomin da ke da alaka da su, da su bi ma’aikatu da hukumomin gwamnati, domin kwato kudaden tare da tura su asusun baitul-mali.
- Majalisa Ta Ba Wa Shugaban NNPCL Awa 24 Ya Bayyana Gabanta Ko Ta Sa A Kamo Shi
- Kwankwaso Ya Soki Gwamnatin Tinubu Kan Ware Arewacin Nijeriya A Rabon Arzikin Ƙasa
Wannan ya biyo bayan kudirin da dan majalisa mai wakiltar Bamidele Salam ya gabatar a ranar Talata, bisa sakamakon binciken da kwamitin kula da asusun gwamnati (PAC) ya yi, a yayin nazarin rahoton shekara-shekara na mai babban binciken kudi na shekarun da suka kare a ranar 31 ga Disambar 2019 da kuma 31 ga watan Disambar 2020, ciki har da binciken da ya shafi gazawar cikin gida da kuma gazawar gwamnati.
Dangane da matakin tsayiwar daka na majalisar, shawarwarin da aka amince na nufin tabbatar da bin doka ta hanyar bayar da umarnin kwato kudaden jama’a da kuma sanya takunkumi a wurin da ya zama wajibi a sanya.
Daga cikin cibiyoyin da aka ayyana wajen yin binciken a 2019, akwai ma’aikatar harkokin wajen kasar, inda aka same tad a laifin kashe kudade ba tare da izini ba, kan aikin masaukin shugaban kasa a ofishin jakadancin Nijeriya da ke Habasha.
Kwamitin ya nemi a mayar da sama da Naira miliyan 124, kusan dala 795,000 zuwa asusun gwamnatin tarayya, an kuma bayar da karin wasu kudade da suka hada da Naira miliyan 31.7 da dala 155,923.00, a matsayin wadanda aka kashe ba bisa ka’ida ba.
An umarci ma’aikatar da ta kwato Naira miliyan 49.4 da aka biya, domin yin gyaran ba tare da bin ka’idojin sayen kayayyakin ba. Kazalika, an raba Naira miliyan 9.2 ga jami’an ofishin jakadancin, ba tare da cikakkiyar shaida ba.
Haka nan kuma, an binciki bankin noma; kan basussuka kimanin Naira biliyan 75.6.
Kwamitin ya umarci hukumar da ta buga jerin sunayen wadanda ake bi bashi a akalla a jaridu guda uku na wannan kasa tare da yin kira ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawar da su kwato wadannan makudan kudade.
Haka nan, dole ne a kwato karin Naira miliyan 350; kana kuma a gabatar da shedu cikin kwanaki 90.
Sannan, an umarci hukumar kula da gidajen yari ta Nijeriya da ta dawo tare da tura Naira miliyan 7.47 na harajin da ba ta biya ba.
Haka zalika, an umarci hukumar kula da fitar da kayayyaki ta Nijeriya (NEPZA), da ta kwaso motoci takwas na hukumar tare da tabbatar da dawo da guda hudu da ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari ta rike ba bisa ka’ida ba.
An kuma bayyana (NEPZA) da laifin karkatar da sama da Naira miliyan 12 tare da sanya takunkumi ga jami’in da kula da harkokin kudi.
An gurfanar da Karamar Hukumar Kwali da ke babban birnin tarayya gaban kuliya, bisa zargin biyan kudi kimanin Naira miliyan 82 da aka raba wasu mutane su 105 da ba a san ko su wane ne ba.
Kazalika, an bukaci tsohon shugaban majalisa day a dawo da kudade zuwa asusun gwamnatin tarayya tare da wasu shaidun day a mika wa kwamitin.
Haka nan, an umarci hukumar kwastam ta Nijeriya da ta yi aiki tare da Akanta Janar na Tarayya, domin samar da cikakken jerin dukkannin abubuwan da aka bai wa asusun tarayya da wadanda ban a tarayya, don tabbatar da hakikanin kudaden da ake da su.
A hukumar samar da wutar lantarki ta karkara kuma, an bankado badakalar kudi sama da Naira biliyan 1.3.
Haka nan, an umarci tsohon manajan darakta da ya mayar da Naira miliyan 394 da ya batar kan ayyukan wutar lantarki da hukumar tattalin arziki ta kasa ta amince da shi.
Bugu da kari, akwai kuma kudaden da suka hada da Naira miliyan 4.2 da aka kashe wajen aiwatar da tallace-tallace, ba a kan ka’ida bad a kuma canza Naira miliyan 969 zuwa Yuro, shi ma ba a kan ka’ida ba, tare kuma da ba da shawarar daukar matakan ladabtarwa ga jami’an da ked a alhakin gudanar da ayyukansu.
An samu kungiya kula da dabbobi ta Nijeriya da badakalar kudaden haraji na duti da kuma sauran kudaden haraji da suke karba.
An bai wa kungiyar umarnin dawo da Naira miliyan 1.1 na harajin dutin daga hannun ‘yan kwangila tare da kuma dawo da sama da Naira miliyan 19 na wasu kudade.
Yayin da majalisa ke karbar rahoton kwamitin, ta yi kira ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa daban-daban da suka hada da EFCC, ICPC da FIRS da su kwato wadannan kudade.
Kwamitin ya kuma kara jaddada bukatar gaggauta bai wa shugabannin hukumomi damar nada masu binciken kudi daga waje, inda kuma ya bayar da shawarwarin yin gyara ga ka’idojin kudi ko wata takardar da sakataren gwamnatin tarayya zai bayar.
Mataimakin kakakin kajalisar, Rt. Hon. Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman majalisar tare da sauran ‘yan majalisa, sun yaba wad an majalisa Salam da sauran ‘yan kwamitin, bisa ga kwazon da suka nuna wajen samar da wannan cikakken rahoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp