Asusun Bunkasa Aikin Noma na Kasa (NADF), da Hukumar SRRBDA da kuma OCP ta Afirka, sun yi hadaka tare da kaddamar da hektar noma 50, domin yin noma na tsawon shekara daya a Dam din Sabke da ke Jihar Katsina.
Amfanin gona kala hudu ake sa ran nomawa a cikin wannan kakada, wadanda suka hada da; Masara, Dawa, Waken Soya da kuma Farin Wake.
- ADC Ga Tinubu: Ina Wutar Lantarki Ta Awa 24 Da Ka Yi Wa ‘Yan Nijeriya Alkawari?
- Sin Da EU Suna Kokarin Samun Moriyar Juna A Shekaru 50 Masu Zuwa
A cikin sanarwar da Asusun ya fitar ya bayyana cewa, za a noma wadannan amfanin ne a fannin noma, domin samun riba.
Babban Sakaren Asusun, Mohammed Ibrahim ya bayyana hakan ne a jawabinsa a wajen rattaba hannun yarjejeniyar gudanar da aikin.
Ya bayyana cewa, za a gudanar da aikin, biyo bayan sakamakon dabarun hadakar da aka kulla; domin fara yin aikin noman, wanda za a yi har zuwa zagayowar wani watan na damina.
Ya sanar da cewa, manufar aikin ta faro ne, biyo bayan wata ziyarar aiki da Asusun ya ka Jihar Katsina.
“Asusun na NADF, ya dauki kwararan matakai; musamman ta hanyar zuba kudade don yin amfani da Dam din na Sabke da ke Jihar Katsina, domin yin amfani da ruwan da ke cikin Dam, don yin noma na zamani“, in ji Mohammed.
“OCP na Afirka, na da kwararru wadanda tuni suka auna yanayin kadadar da a gudanar da aikin, musamman duba da cewa; za a iya yin amfani da ruwan Dam din na Sabke, wajen gudanar da aikin”, a cewarsa.
Ya kara da cewa, Bankin shi kuma zai samar da wadatattun kudaden da za a yi aikin, wanda kuma Asusun na NADF zai kasance mai sanya ido kan aikin.
Ya kuma bayyana gamsuwar cewa, aikin zai kasance na zamani.
Shi kuwa a nasa jawabin, Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Radda ya sanar da cewa; gwamnatinsa za ta bai wa aikin goyon bayan da ya dace.
“A lokacin da aka gabatar min da batun wannan aiki, nan da nan na aminta da shi, duba da irin dimbin alfanun da ke tattare da aikin, musamman wajen kara bunkasa tattalin arzikin Jihar Katsina da kuma rayuwar ‘yan jihar baki-daya“, in Radda.
“Burinmu shi ne, muga ana yin noma har zuwa gazayowar wata daminar a jihar, musamman domin al’ummarmu su kasance cikin shiri wajen gudanar da ayyuka a koda-yaushe tare kuma da amfana daga kudaden da aka kashe wajen sake gyaran wannan Dam da aka yi watsi da shi a baya”, a cewar gwamnan.
Shi kuwa a nasa bangaren, wakilin OCP na Afirka; Alik Orebaoghene ya sanar da cewa; gonar za ta kasance wajen bayar da horon sanin makamar aikin noma, musamman a tsakanin kananan manoma da ke jihar.
A karkashin wannan hadaka, ana sa ran OCP na Afirka zai samar da ingantaccen takin zamanin da za a gudanar da wannan aiki.
Shi ma, Manajan Daraktan Hukumar SRRBDA; Abubakar Malam, a nasa jawabin, jinjina ya yi kan kokarin da aka yi na sake farfado da wannan aiki.
Ya sanar da cewa, bisa tsarin kudurin Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu (Renewed Hope Agenda), muna alfahari da samar da hektar noma daidai har guda 50, domin aiwatar da wannan aiki; musamman domin kara samar da wadataccen abinci a wannan kasa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp