Mutuwa yayin ko bayan saduwa da iyali lamari ne da bincike ya karanta a kai kwarai da gaske, hatta kuwa a kasashen Turai, saboda kiyaye sirri.
Amma kuma ga dukkanin alamu, lamarin yana ci gaba da kara yawaita a tsakanin al’ummar, musamman a kasashen Afirka da sauran sassan duniya baki-daya.
Har ila yau, hadarin mutuwa yayin ko bayan saduwa da iyali, yana da alaka da abubuwa da dama kamar haka:
1- Matsanancin motsa jiki, wanda ake bukata a yayin saduwa da iyali.
2- Shan magungunan kara karfin namiji, wadanda likitoci suke bayarwa.
3- Shan miyagun kwayoyi, jike-jiken magungunan karfin maza da sauran nau’o’in kayan karfin maza da ake amfani da su yau da kullum.
Don haka, akwai bukatar a lura da hadarin da zuciya take shiga; bayan shan ire-iren wadannan magunguna na karfin maza.
A nan, ana tursasa zuciya ne tare kuma da tunzura ta ta yi aiki tukuru fiye da ikon da take da shi na lafiyarta, wanda hakan ko shakka babu, zai haifar mata da gagarumar matsala.
Haka zalika, bugun zuciya yana kara sauri tamkar gudun doki, jini kuma yana hauhawa fiye da lafiyayyen hawa yayin saduwa da iyali.
Kazalika, bugun numfashi yana karuwa; domin musayar iska fiye da ikon lafiyar da huhu da jijiyoyin jinni suke da shi, sannan kuma tsokokin jiki suna yin yunkuri fiye da ikonsu.
Saboda haka, idan kuwa har za a tursasa wa zuciya yin aiki fiye da ikon da ta take shi, hakan na iya durkusar da ita har ta tsaya da aiki kwata-kwata. Wannan shi ake kira da bugun zuciya (Heart attack) a turance. Galibi, bugun zuciya yana zarcewa ne zuwa ga mutuwa nan take, ba tare da wani bata lokaci ba.
Ga wadanda shekarunsu suka mika kuwa, abin da jiya ta yi; tabbas ba lallai ba ne yau ta yi ba. Shekaru suna tafiya ne kafada da kafada da lafiyar jikin Dan’adam.
Saboda haka, hadarin mutuwa yayin saduwa da iyali bayan shan magungunan karfin maza da sauran makamantansu, yana karuwa ne da mikawar shekaru.
Daga karshe, saduwa da iyali yana bukatar aikin zuciya, jini, huhu da kuma sauran tsokokin jiki. Atisaye ko motsa jiki, su ne ingantacciyar hanyar bunkasa ayyukan zuciya, jini, huhu da kuma tsokokin jiki.
Bugu da kari, atisaye yana taimaka wa bunkasa karfi da juriyar wadannan sassan jiki da ake bukatar su, yayin saduwa da iyali a koda-yaushe.
Har ila yau, a yi kokari a fara atisaye a-kai-a-kai, domin fara yin bankwana da shaye-shayen ire-iren magungunan karfin maza, domin kuwa, zabin lafiyarka shi ne zabin rayuwarka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp