ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Amfanin Zogale Ga Lafiyar Jikin Ɗan’adam

by Sani Anwar
9 months ago
Zogale

Masana harkokin lafiyar abinci, sun bayyana amfanin da ganyen zogale ke da shi a jikin Ɗan’adam, sakamakon sinadarin da yake ƙunshe da su.

Har ila yau, bincike ya tabbatar da cewa; zogale yana da matuƙar albarka, domin kuwa ya kan fito har a wurin da babu ruwa.

  • Kasar Sin Ta Zama Babbar Kasuwar Da Fim Din “Zootopia 2” Ya Samu Kudi
  • Farfesa Gwarzo Ya Gwangwaje Cibiyar Ilimi ‘Alliance Française Kano’ Da Gini Mai Hawa Biyu Na Zamani

Don haka, ganyensa da sassaƙensa; na da matuƙar amfani a jikin mutum. Sannan kuma, yana ɗauke da sinadarin A.B.C.D har ma da E, kana kuma yana ɗauke da sinadarin calcium da potassium, kazalika kuma; mansa yana cikin mayukan da suka fi tsada a duniya.

ADVERTISEMENT

Kazalika, akwai magunguna 18 da zogale ke yi ga lafiyar Ɗan’adam kamar haka:

-Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi, domin maganin Olsa (Ulcer).

LABARAI MASU NASABA

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”

2 – 3 Cikin 10 Na Masu Cutar Diphtheria Na Iya Mutuwa A Katsina – NMA

-Ana kuma shafa ɗanyen ganyen zogale a kan goshi, don maganin ciwon kai.

-Haka nan, ga wanda ya ji wani rauni ko sara; idan ya shafa ɗanyen ganyen zogale, jinin zai tsaya nan take da izinin Allah.

-Ga mai fama da ƙurajen jiki, sai ya haɗa garin zogale da man zaitun; ya riƙa shawa.

-Ana kuma zuba garin zogale a kan gyambo ko wani rauni, domin ya yi saurin warkewa.

-Sanya garin zogale a cikin abinci, na maganin hawan jini da kuma ƙara wa mutum kuzari,

-Ana dafa ganyen zogale, a saka kanwa ‘yar kaɗan; don maganin shawara.

-Ga mai fama da ciwon ido, zai riƙa ɗiga ruwan ɗanyen zogale; haka nan, shi ma mai fama da ciwon kunne.

-Macen da ke shayarwa kuma, sai ta dafa furen zogale da zuma; domin samun ƙarin yawan ruwan nono.

-Wanda ke fama da yawan fitsari ko ciwon Siga, sai ya riƙa shan furen zogale da citta kamar shayi.

-Kazalika, cin zogalen ma a haka; na maganin tsutsar ciki, musamman ga yara ƙanana.

-Ana daka ganyen  zogale da ‘ya’yan ɓaure a sha da nono ko kunu, domin kuwa yana maganin ciwon hanta.

-Ga mai fama da sanyin ƙashi ko wani kumburi, sai ya soya ‘ya’yan zogale ya daka su; ya kuma haɗa da man kwakwa (man- ja) sai ya riƙa shafawa.

-A daka zangarniyar zogale da ‘ya’yan da ke ciki da kaninfari, citta, masoro da kuma kimba, domin ƙarin ƙarfin namiji, sannan yana ƙara wa mata nishaɗi.

-A daka saiwar zogale da ‘ya’yan kankana a sha a nono, yana maganin tsakuwar ciki (Apendis).

-Haka nan, yana maganin typhoid, maleriya, basir da shawara; ta hanyar yawan shan ruwan dafaffen zogale.

-Kazalika, zogale na rage raɗaɗin ciwon HIV ta hanyar shan dafaffen ruwan zogalen.

Zogale
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    2027:Mata Shida Da Ke Takarar Neman Shugabancin Nijeriya
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Dambarwa A Kasuwancin Iyalan Indimi
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Illar Shan Taba Sigari Da Dangoginta

MASU ALAKA

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”
Manyan Labarai

Yadda Na Tsira Daga Cutar Mashaƙo A Katsina: “Na Fara Da Tsartuwar Jini Tare Da Yawu”

September 3, 2026
Zogale
Kiwon Lafiya

2 – 3 Cikin 10 Na Masu Cutar Diphtheria Na Iya Mutuwa A Katsina – NMA

August 30, 2026
Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?
Kiwon Lafiya

Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?

August 29, 2026
Next Post
Harin Ƴan Bindiga Ya Halaka Mutum 11 A Pretoria

Harin Ƴan Bindiga Ya Halaka Mutum 11 A Pretoria

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.