Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya ce Sin na kira ga dukkanin sassan kasa da kasa, da su ci gaba da himmatuwa wajen warware rikicin kasar Ukraine ta hanyar lumana. Ya ce kamata ya yi Amurka ta ji kunyar zargi marar tushe da ta yi wa kasar Sin, yayin zaman kwamitin tsaron MDD na makon nan.
Geng, ya ce a baya-bayan nan kasashen Rasha da Ukraine, sun ci gaba da aiwatar da sakamakon da aka cimma, a jerin zaman shawarwari da aka gudanar a baya, da musayar firsinonin yaki, da ma gawawwakin sojojin da suka rasu a filin daga.
- Gwamnatin Tarayya Ba Ta Soke Jarabawar WAEC Da NECO Ba
- ‘Yancin Gashin Kai: Ma’aikatan Kananan Hukumomi Sun Yi Barazanar Shiga Yajin Aiki
Jami’in ya shaidawa zaman taron kwamitin tsaron majalisar cewa, Sin na maraba da ci gaban da aka samu, tana kuma kira ga dukkanin sassa da su ci gaba da azamar wanzar da zaman lafiya, da ci gaba da samar da matsaya guda, da inganta amincewa da juna, ta yadda za a kai ga cimma cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa wadda za a aiwatar da ita yadda ya kamata.
A daya bangaren kuma, Geng Shuang ya yi watsi da zargin da Amurka ta yi wa kasar Sin, na cewa wai Sin na fitar da kayayyakin da ake iya amfani da su a ayyukan soji da na fararen hula ga Rasha. Ya ce, Sin ba ta taba samar da makamai masu hadari ga sassan dake dauki ba dadi da juna ba, kuma har kullum tana kayyade fitar da irin wadannan kayayyaki, ciki har da jirage marasa matuka.
Daga nan sai ya yi kira ga Amurka, da ta dakatar da zargin da take yi wa Sin dangane da batun Ukraine, da kokarin haifar da fito-na-fito, maimakon haka, ta zage damtse wajen aiwatar da matakan ingiza dakatar da bude wuta, da tattaunawar zaman lafiya.
Ya ce, a cikin mako guda, Amurka ta yi zarge-zarge da dama marasa tushe kan kasar Sin, a lokutan zaman kwamitin tsaron MDD, wanda hakan ya shaida cewa, burinta ba wai na ganin an wanzar da zaman lafiya da tsaro, ko yayata bukatar warware rigingimu, ko kawo karshen yaki ba ne, maimakon haka, Amurka na amfani da dandalin kwamitin tsaron ne wajen kaiwa wasu sassa hari, ko yunkurin dakile ci gabansu, tare da amfani da dabarun siyasa don cimma burikanta na kashin kai. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp