Kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ya sanar da korar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, daga jam’iyyar, tare da hana shi duk wata hulɗa da jam’iyyar na tsawon shekaru 30 masu zuwa.
A cewar kakakin jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Rufus Araba Aiyenigba, an ɗauki matakin ne bayan gudanar da bincike mai zurfi dangane da zargin cewa El-Rufai ya ƙirƙiri takardun shaidar zama ɗan jam’iyyar, tare da ƙoƙarin karkatar da harkokin cikin gida ta hanyar yaudara da dabara mara tsari.
- Rikici Ya Turnuke Jam’iyyar SDP A Yayin Da Aka Samu Shugabanni Bangare Biyu A Kogi
- Ra’ayoyin PDP, PRP Da SDP Kan Gudanar Da Zabe A Kano
Aiyenigba ya bayyana cewa El-Rufai bai taba yin rajista da SDP a matakin mazaɓarsa ba kamar yadda kundin tsarin jam’iyyar ya tanada, amma ya sanar da jama’a a kafafen sada zumunta cewa ya shiga jam’iyyar, har ma ya ɗauki hoto da wasu jiga-jigan jam’iyyar da aka dakatar domin ƙarfafa wannan iƙirarin.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa duk da an nuna masa karamci sakamakon Muƙaminsa na baya a matsayin minista da gwamna, bincike ya tabbatar cewa bai cika sharuɗɗan zama mamba ba. A maimakon haka, yana ƙoƙarin mamaye jam’iyyar ne tare da wani shiri da ke haɗe shi da wata jam’iyya daban.
Har ila yau, SDP ta zargi El-Rufai da nuna gaba da jam’iyyar lokacin da yake kan mulki a ƙarƙashin APC da kuma yunƙurin amfani da SDP wajen cika burinsa na siyasa, duk da kasancewarsa da wata jam’iyyar daban (ADC).
Jam’iyyar ta buƙaci hukumar INEC da sauran hukumomi da su lura cewa El-Rufai ba ɗan jam’iyyar ba ne, kuma bai da hurumin wakiltar ta a kowanne mataki. SDP ta kuma jaddada ƙudurinta na kare dimokuraɗiyya ta cikin gida da kuma adawa mai tushe da gaskiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp