Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya sauke Farfesa Muhammad Sani Bello daga matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai kuma memba na majalisar zartarwa ta jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Malam Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Talata, an bayyana cewa Ahmed Maiyaki, wanda shi ne Manajan Darakta na Kamfanin Yaɗa Labarai na Kaduna (KSMC), ne za a maye gurbinsa.
- Sin Da Benin Da Thailand Za Su Aiwatar Da Matakan Saukaka Tantance Kaya Na Kwastam
- Babu Wata Karamar Hukumar Da Ke Ƙarƙashin Ikon Ƴan Ta’adda A Filato -Gwamna Mutfwang
Gwamna Sani ya gode wa Farfesa Bello bisa ayyukan da ya gudanar, inda ya ce shi ne kwamishinan ilimi na farko a gwamnatinsa, kafin daga baya ya zama kwamishinan yaɗa labarai.
Ya kuma yi masa fatan alheri a sauran harkokinsa na gaba.