Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng, ya yi kira ga kasar Amurka da ta yi aiki tare Sin wajen kyautata cimma matsaya guda, da rage sabani, da karfafa hadin gwiwa, da zurfafa shawarwari da tuntuba, tare da kara azamar cimma karin moriyar bai daya tsakanin sassan biyu.
He Lifeng, ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yana mai cewa wanzar da daidaito, da yanayi mai kyau, kuma mai wanzuwa a fannin raya tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, ba kawai zai haifar da ci gaban muradun sassan biyu ba ne, har ma zai bayar da gudummawa ga bunkasa, da daidaiton tattalin arzikin duniya baki daya.
- Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
- ’Yansanda Sun Gano Gawar Ɗan Jaridar Da Aka Kashe A Jihar Kogi
He ya yi tsokacin ne yayin sabon zagayen tattaunawar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka, wanda ya gudana tsakanin ranakun Litinin zuwa Talata a birnin Stockholm na Sweden, inda sakataren baitul-malin Amurka Scott Bessent, da wakilin cinikayya na Amurka Jamieson Greer suka jagoranci bangaren Amurka.
Yayin zaman tattaunawar, sassan biyu sun zurfafa shawarwari, da musayar ra’ayoyi masu ma’ana, game da alakar kasashen biyu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, da manufofin lura da gudana da ci gaban tattalin arziki, da sauran batutuwan cinikayya da tattalin arzikin dake janyo hankulansu.
Bisa sakamakon zaman, sassan biyu sun amince da tsawaita adadin kwanaki 90 da aka tsayar, na dakatar da karin harajin ramuwa da Amurka ta dora kan hajojin Sin dake shiga kasar kan kaso 24 bisa dari, da kuma dakatar da matsayar Sin ta daukar matakan martani kan harajin.
A nata bangare kuwa, Amurka ta bayyana aniyarta ta aiki tare da bangaren Sin, wajen ci gaba da warware sabani a fannonin tattalin arziki da cinikayya ta hanyar tsarin gudanar da shawarwari, da ingiza damar samar da karin nasarori daga tattaunawar, da kara samar da daidaito a alakar tattalin arziki da cinikayya tsakaninta da Sin.
Wakilin cinikayya na kasa da kasa na Sin karkashin ma’aikatar cinikayya, kuma mataimakin ministan cinikayyar kasar Li Chenggang, ya bayyana a yayin da yake yiwa manema labarai karin haske game da zaman tattaunawar sassan biyu. Ya ce sassan biyu suna sane da muhimmancin wanzar da daidaito, da kyautata alakar tattalin arziki mai nagarta tsakanin Sin da Amurka, sun kuma yi kyakkyawar musaya game da muhimman batutuwan cinikayya da na raya tattalin arziki dake jan hakulansu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp