Tauraron dan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen, ya kammala komawarsa ƙungiyar Galatasaray ta ƙasar Turkiyya daga Napoli, a wata yarjejeniya ta dindindin da ta kai Yuro miliyan 75. Ƙungiyar Galatasaray ta sanar da kammala ɗaukar Osimhen a shafinta na yanar gizo a ranar Alhamis, inda ta bayyana cewa yarjejeniyar ta fara aiki daga nan take.
Ɗan wasan mai shekaru 26 ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekaru huɗu tare da zakarun na ƙasar Turkiyya, kuma za a biya shi Yuro miliyan 15 a kowace kakar wasa. Hakazalika, zai karɓi ƙarin Yuro miliyan 5 a matsayin hakkinsa na mallakar hoto, yayin da Napoli za ta sami kashi 10 cikin 100 na duk wani kudi da za a sayar da shi da shi nan gaba.
- Napoli Ta Nada Antonio Conte A Matsayin Sabon Kocinta
- De Bruyne Ya Kammala Komawa Napoli Bayan Barin Man City
A cikin yarjejeniyar, an haramtawa Osimhen sake komawa wata ƙungiya daga Serie A ta Italiya na tsawon shekaru biyu masu zuwa. Yayin da yake jawabi bayan sanya hannu, Osimhen ya bayyana farin cikinsa da dawowa cikin ƙungiyar Galatasaray. “Ina godiya ga shugaban kulob ɗin da mataimakinsa bisa wannan dama. Ina alfahari da kasancewa a cikin wannan babban gida,” in ji shi.
Osimhen ya yi kyakkyawan aiki a kakar da ta gabata inda ya zura ƙwallaye 37 tare da taimakawa aka zura ƙwallo 8 a wasanni 41 da ya buga. Wannan sanarwar na zuwa ne daidai lokacin da ake ta rade-radin saɓani tsakaninsa da Napoli, wanda yanzu haka an rufe batun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp