ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, July 11, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Shekara 2 Ta Gwamnatin Tinubu: Gwamnonin Arewa Sun ƙaryata Zargin ACF Na Watsi ɗa Yankin

by Rabi'u Ali Indabawa
11 months ago
Gwamnati

Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta shiga halin ni-ƴa-su bayan da ƙungiyar tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta zarge ta da mayar da yankin saniyar ware a wani taro da ta gudanar ranar Litinin.

Sai dai gwamnonin jihohin Arewa da fadar shugaban ƙasa sun gaggauta yin tir da wannan ikirari tare da tabbatar da cewa yankin ya samu ci gaba ta fusar samar da ababen more rayuwa da sauye-sauyen manufofin da ke amfanarwa.

Wazirin ɗutse kuma shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar ACF, Alhaji Bashir ɗalhatu ne ya yi wannan iƙirari a taron tattaunawa na kwana biyu kan harkokin gwamnati da jama’ar ƙasa wanda gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello (SABMF) ta shirya a Arewa House Kaduna.

ADVERTISEMENT

Ya yi zargin cewa Arewa ba ta samun wata kulawa duk da bayar da gudunmawar sama da kashi 64 na ƙuri’un da suka kai Tinubu kan karagar mulki a 2023.

  • ACF Ta Nemi Rundunar Soji Ta Sake Dabarun Yakinta, Bayan Luguden Wutar Silame
  • Cikin Wata 2 Ƴansanda Sun Damƙe Mutane 5,488, Sun Ceto 170 Da Aka Sace

ɗalhatu ya koka da cewa, kusan shekaru biyu a mulkin Tinubu, yankin na ci gaba da fama da matsalar rashin tsaro, rashin ababen more rayuwa, ƙarancin kuɗi, noma, da matsalar ilimi. A cewarsa, bambancin rabon ayyukan na ƙara bayyana kuma yana sanya ayar tambaya kan ƙudirin gwamnatin na samar da daidaito a yankin.

LABARAI MASU NASABA

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

Ya nuna rashin jin daɗinsa da rabon ayyukan tituna kamar yadda aka samu a cikin wata sanarwa da ma’aikatar ayyuka ta fitar a watan Mayun 2025, wanda a cewarsa, an ware Naira tiriliyan 1.394 wa yankin Kudu-maso-Yamma, yayin da ɗaukacin yankin Arewa-maso-gabas suka samu Naira biliyan 30, sai kuma yankin Arewa-maso-Yamma Naira 105 biliyan.

“Rashin tsaro ya zama babban abin damuwa, ƴan fashi, tada ƙayar baya, da kuma garkuwa da mutane na ci gaba da wanzuwa a sassan Arewa da dama, inda jihohi kaɗan ne kamar Kaduna da Bauchi suka samu kwanciyar hankali,” in ji shi.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fito da manufofin siyasa don kawo ƙarshen rikicin.

ɗalhatu ya kuma soki manufofin gwamnatin tarayya kan harkokin noma, inda ya ce sun jawo ce-ce-ku-ce a harkar noma a cikin gida, sakamakon ƙaruwar shigo da abinci daga ƙasashen waje, lamarin da ya sa aka rufe wasu masana’antun shinkafa a yankin. Ya yi gargaɗin cewa irin waɗannan manufofin suna raunana ƙashin bayan tattalin arzikin yankin.

Ya ƙara da nuna damuwa game da giɓin da ake samu na wutar lantarki a yankin, ya kuma buƙaci shugaba Tinubu ya kafa dokar ta-ɓaci a fannin wutar lantarki. Ya buƙaci a gaggauta kammala wasu muhimman ayyukan makamashi kamar madatsar ruwa ta Mambilla da bututun iskar gas daga Abuja zuwa Kaduna da Kano, waɗanda a cewarsa, suna da matuƙar muhimmanci ga makomar masana’antun Arewacin Nijeriya.

A ɓangaren ilimi kuwa, ɗalhatu ya buga misali da bayanan bankin duniya da ke nuni da cewa kashi 80 cikin 100 na yara miliyan 20 na Nijeriya da aka ƙiyasta ba sa zuwa makaranta ƴan Arewa ne. Ya buƙaci gwamnatin Tinubu da ta sake ƙaddamar da shirin ilimi na bai ɗaya (UBE) tare da himma wajen da mai da hankali kan ilimi kyauta.

Ya kuma yi tir da taɓarɓarewar ababen more rayuwa na kiwon lafiyar al’umma, da sake ɓullar cututtuka, da yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasan Arewa, inda ya yi kira da a gaggauta ɗaukar matakin na gwamnatin tarayya a fannonin kiwon lafiya na matakin farko, da sarrafa magunguna, da samar da ruwan sha.

Ya bayyana tafiyar hawainiyar da ake yi a kan aikin kamfanin tama da ƙarafa na Ajaokuta a matsayin abin takaici, ya kuma yi gargaɗin a kan dogaro da ƙawancen jama’a da masu zaman kansu (PPP) fiye da kima wajen samar da irin waɗannan kadarorin.

ɗalhatu ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna ɓangaranci, son zuciya, da rashin sanin halin da Arewa ke ciki.

Hausawa na Karin magana cewa “Gyara kayanka ba ya zama sauke mu raba,”. Ya ba da shawarar sake farfaɗo da kwamitin tuntuɓar gwamnatin tarayya domin zurfafa tattaunawa.

Sai dai kuma a wani martani da ya mayar, Shugaban ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa (NSGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce Shugaba Tinubu ya cika alƙawuran da ya ɗaukar wa Arewa kuma yana ci gaba da aiwatar da ajandarsa ta ‘Renewed Hope’

Gwamna Yahaya ya ce tarurrukan da suka haɗa da ƙungiyar SABMF na da matuɗar muhimmanci wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya da tabbatar da bin doka da oda, amma ya jaddada cewa shaidun da ke ƙasa na nuna ci gaba mai ma’ana a sassa daban-daban na faɗin yankin.

“Lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya yi yaƙin neman zaɓe a faɗin Arewa a shekarar 2023, ya yi alƙawuran da ya dace, a yau muna ganin cikarsu ta hanyar ayyukan da aka kammala da kuma waɗanda ke ci gaba da gudana,” in ji Yahaya, inda ya ƙara da cewa an samu gagarumin ci gaba a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano, layin dogo na Kano-Katsina-Maradi, gyaran matatar mai ta Kaduna, da kuma bunƙasa man fetur na Kolmani.

Yahaya lauded the newly established Ministry of Liɓestock ɗeɓelopment, calling it a major step towards modernising pastoral systems in the region.

Ya kuma bayyana cewa an samu ci gaba a harkokin tsaro a jihohi da dama, inda ya yi nuni da yadda aka kawar da shugabannin ta’addanci da ƴan fashi sama da 300.

Yahaya ya yaba wa sabuwar ma’aikatar kula da kiwon dabbobi da aka kafa, inda ya bayyana hakan a matsayin wani babban mataki na zamanantar da tsarin kiwo a yankin.

A cewarsa, sabbin ababen more rayuwa na tituna da na dogo, inganta kiwon lafiya, ayyukan noma, da kuma ɗaukar matakan da suka dace a fannin ilimi, musamman kan matsalar Almajirai da yaran da ba su zuwa makaranta, na nuni da dabarun da gwamnatin tarayya ta yi domin ɗaukaka yankin.

A nasa jawabin, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume, wanda ya wakilci Shugaba Tinubu, ya nanata ƙudurin Shugaban ƙasa na samar da ci gaba mai amfani, yana mai bayyana cewa “ba wani yanki da za a barI baya.

Akume, wanda ya jagoranci tawagar ministoci, shugabannin hukumomi, da mataimakan shugaban ƙasa a wajen taron, ya ce ajandar Renewed Hope an kafa ta ne a kan ginshiƙan daidaito, shiga tsakani, da kuma gaskiya.

Ya zayyana muhimman ayyukan da ake gudanarwa a Arewa da ma faɗin ƙasar nan.

Ya ambaci babbar hanyar Legas zuwa Calabar, babbar titin Sokoto-Badagry, Kano-Maradi da Fatakwal-Maiduguri, da ayyukan gina gidaje da na noma da dama a matsayin shaida na ayyukan gwamnati.

Akan sake fasalin tattalin arziki, Akume ya ce cire tallafin man fetur da kuma haɗewar farashin canji abu ne mai zafi amma an yi su a matakan da suka dace domin daidaita tattalin arzikin ƙasar.

Ya bayyana cewa an riga an bayar da sama da Naira biliyan 53 ta tsarin bayar da lamunin rancen ɗalibai don cin gajiyar ɗaliban manyan makarantu sama da 400,000 a faɗin ƙasar nan.

Akume ya ce Tinubu ya ɗau turbar kai Nijeriya matsayin da ya yi alƙawri, inda ya ƙara da cewa.

“Zan buƙaci ƴan siyasa daga yankin Arewa da su jira har zuwa 2031. Kada ku shiga ƙungiyar da za ta haifar da lalata ci gaba daban-daban da Shugaba Tinubu ya samu. Shugaban ƙasa ya taɓa dukkan sassan ƙasar nan da kowane ɗan ƙasa.”

Ya kuma jinjinawa marigayi Firimiyan Arewacin NIjeriya, Sir Ahmadu Bello, inda ya bayyana shi a matsayin ɗan siyasa mai wakiltar haɗin kai, hangen nesa, da gudanar da mulki na bai ɗaya. Ya kuma yaba da gudunmawar da wasu fitattun shugabannin Arewa suka bayar da suka haɗa da Cif Solomon Lar da Malam Adamu Ciroma.

Waɗanda suka yi wa ƙasa hidima da tsaffin gwamnonin Arewa, ministoci, masu ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Malam Nuhu Ribadu, Shugaban ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa Sanata George Akume, shugabannin gargajiya, shugabannin MɗA na tarayya, shugabannin tsaro, da shugabannin masana’antu ne suka hallarci taron.

Gwamnati
Rabi'u Ali Indabawa
+ postsBio
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Adadin Mutanen Da Tsananin Zafi Ya Kashe A Turai Ya Haura Dubu 1,300 —WHO
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Pakistan Ta Kashe Mutum 36 A Hare-haren Da Ta Kai Kan Iyakarta Da Afghanistan
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Dalilanta Na Sake Fasalin Hukumar NYSC
  • Rabi'u Ali Indabawa
    https://hausa.leadership.ng/author/rabiu-ali-indabawa/
    Sarkin Zazzau Ya Umarci A Soke Wasu Al’adu Da Ke Kawo Wa Aure Cikas

MASU ALAKA

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta
Manyan Labarai

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya
Manyan Labarai

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

July 11, 2026
2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa
Da ɗumi-ɗuminsa

2027: Tinubu Ya Sake Zaɓar Shettima A Matsayin Abokin Takararsa

July 10, 2026
Next Post
Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447 Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa

Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447 Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa

LABARAI MASU NASABA

Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Dole Mata Su Rungumi Sana’o’i Domin Tsira Daga Takaicin Zamani —Ramatu Bello

July 11, 2026
Gwamnati Ta Shirya Gina Gidaje 20,000 Duk Shekara Haɗin Gwuiwar  Jamus

Gwamnati Ta Shirya Gina Gidaje 20,000 Duk Shekara Haɗin Gwuiwar Jamus

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ra’ayin Al’umma Game Da Shirin Gwamnati Na Sake Fasalin Hukumar NYSC

July 11, 2026
Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

Mutum 1 Ya Mutu, 7 Sun Jikkata Yayin Da Ginin Majalisar Dokokin Gombe Ya Rufta

July 11, 2026

Ronaldo Da Ƴanwasan Da Suka Buga Kofin Duniya Na Ƙarshe A Rayuwarsu

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

NDLEA Ta Cafke Ƴar Shekara 67 Da Hodar Iblis Da Aka Ɓoye A Cikin Ayaba

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

July 11, 2026
Labarin Farfesoshi Tagwaye Da Suka Yi Karatun Digiri Tare Suna Aiki Tare A Wuri Ɗaya

Duk Da Faɗuwar Farashin Ɗanyen Mai Ƴan Nijeriya Na Fama Da Tsadar Man Fetur

July 11, 2026
Kasar Sin Ta Fitar Da Shirin Kai Wa Matakin Koli Na Fitar Da Hayakin Carbon

Kasar Sin Ta Fitar Da Shirin Kai Wa Matakin Koli Na Fitar Da Hayakin Carbon

July 10, 2026
Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B

Sin Ta Yi Nasarar Dawo Da Rokar Da Ake Sarrafa Dawowarta A Tashin Farko Na Samfurin Long March-10B

July 10, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.