A halin yanzu dai da yawa ‘yan kasuwa na sane da halin da tattalin arziki yake ciki a kasahen duniya ciki kuwa har da Nijeriya.
Duk da abin da gwamnan babban bankin Nijeriya da ministocin kudi suka sha fada cewa wannan matsalar tattalin arzikin tana shafar Nijerya amma za ta wuce.
Ciniki da kasuwancin a irin wannan lokaci na matsin tattalin arziki shi ma yana jin jiki domin muna ganin abin da yake faruwa a kasashe irin su Amirka,Jafan,Chana,Ingila da sauransu, inda ‘yan kasuwa ke shan wahala saboda jama’a basu da hlin sayen kayayyaki.
Dalili shi ne babu aikin yi, kamfanoni suna sallamar ma’aikata da yawa inda alkaluma suka nuna rabon da a samu irin wannan hali tun lokacin da aka yi yakin duniya na biyu.
To! kasashen da aka ci gaba kenan inda komai yana tafiya dai-dai ba tare da wata matsala ba saboda su ne kasashen da muka dogara da su wajen samar mana da ababan more rayuwa kama daga kayan abinchi har izuwa na tufafi da muhallinmu.
A makonnin da suka gabata na yi rubutu akan kananan sana’oi da yadda suke taimakawa kasa. Shi ne yanzu kuma na ga ya dace na kuma yin wani dogon rubutun akan yadda ‘yan-kasuwa kanana da mtsakaita kai har ma da manyan ya kamata su bi don cin ribar kasuwancin nasu.
Na taba yin wannan rubutu a shekarun baya, amma yanzu da yake abubuwa da yawa sun sauya tun lokacin da na yi wancan rubutun shi ne na ga dacewar na kuma dawo da shi ta inda zan saka canje-canjen da aka samu na abubuwa da yawa da suke faruwa a duniyar kasuwanci a yanzu.
‘Yan kasuwarmu da na kkasashen waje da guguwar tattalin arziki ta shafa suna iya kokarinsu su ga sun tsira da kasuwancinsu. Wannan dalilin ne ya sa na ga ya dace na tunasar da namu ‘yan kasuwar akan abin da yake faruwa ta yadda za su sake tunani da kuma komawa baya don yin bitar abubuwan da suka faru lokacin da komai yake tafiya dai – dai da kuma wannan lokacin da kowa zai iya cewa komai ba ya tafiya dai-dai.
Duk rintsi duk wahala, za’aga akwai wadanda su kuma sai su sha romonsu, to amma wadanda suka fi shan jiki su ne suka fi yawa don haka akwai bukatar na yi amfani da ilimin da Allah ya bani don mu fitar da jaki daga duma.
Mu kuma gode wa Allah da ya raya mu ya bamu lafiya domin mun san ba wani abu muka bashi ba yai mana hakan ni’imarSa ce kawai wacce yake ba wa wanda ya ga dama. Muna kara gode masa.
Abin sha’awa game da ilimi ko na ce fasaha shi ne basu da iyaka. Abin nufi a nan shi ne sanda aka gano wani abu, to a lokacin kuma wani abun zai kuma bullowa shi ya sa shi ilimi kullum sabo ne kuma sanda ka gano wani abun wani kuma ya dade da sanin wannan abin, shi ya sa nake bukatar in ga wani kuskure cikin abin da na rubuta, to don Allah a yi min afuwa domin nima har yanzu koyo nake.
Sannan dalilin da ya sa na ga ya dace na yi wannan rubutu don na wayar da kan al’ummar Nijeriya ne kawai yadda nima zan zamo na ba da tawa gudumawar wajen ci gaban kasata.
Shi dai kasuwanci in ji masana kasuwancin sun ce ”yaki ne” kamar yadda sojoji suke yaki manufarsu itace su kori abokan gaba su kama gurare ya zama su ne suke da ikon wurin. Shi ma dan kasuwa kusan haka yake amma shi dan kasuwa duk burinsa a yakinsa shi ne ya kama mai saye.
Akwai wata halayya ta ‘yan kasuwa wacce a duk lokacin da za ku yi magana akan yaya kasuwa zai ce maka ”to! mun gode Allah” amma fa shi ya fadi hakan ne don kar ka san me yake samu.
Musamman a yi rashin sa’a rokonsa za ka yi ba zai taba nuna maka ai yana cikin jin dadi ba kullum, sai dai ya nuna maka ai kasuwa ba labari ana dai yi ne kawai don kar a zauna haka.
Shin dan uwa, baka san wannan karyar baya take mai da kai ba?.
Ga wata tambaya shin laifi ne ka gaya wa mutum gaskiya cewa yau kasuwa ta yi kyau koda wannan mutumin rokonka zai yi?
Za mu ci gaba a mako mai zuwa, inda za mu kawo muku matakai shida na samun nasara ga ‘yan kasuwa.