• English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sanata Buba Ya ƙaryata Jita-jitar Cewa Majalisa Ta Amince da ƙirƙiro Sabbin Jihohi 12

byHussein Yero
2 months ago
Sanata

Sanata mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta Kudu, Sanata Shehu Buba Umar ya ƙarya labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa Majalisar dattawa ta amince da ƙirƙiro sabbin jihohi guda 12, ya misalta labarin da cewa bai da tushe balle makama. 

da yake ganawa da ƴan jarida a Bauchi ranar Asabar da ta gabata, Buba ya fayyace cewa, a halin da ake ciki dai majalisar ta kafa kwamitocin jin ra’ayin jama’a daga sassa daban-daban har guda shida na ƙasar nan dangane da kwaskwarima ga kundin tsarin mulki na 1999 tare da neman ƙirƙiro sabbin jihohi da ƙananan hukumomi.

Ya tabbatar da cewar a halin yanzu majalisar dattawa ko karɓar rahoton kwamitocin jin ra’ayoyin jama’a ba ta yi ba, balle ta zauna ta tantance ta duba wuraren da suka dace a amince da samar da sabbin jihohi ko ƙananan hukumomi a cikinsu. 

  • Gwamna Ademola Adeleke Ya Ƙaryata Jita-Jitar Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
  • Majalisar Dattawa Za Ta Yi Zama Na Musamman Don Karrama Buhari 

LEADERSHIP Hausa ta rawaito cewa, tun kafin gudanar da taron jin ra’ayin jama’a a shiyyoyi ƙasar nan, majalisar dattawa ta amshi buƙatun neman ƙirƙiro sabbin jihohi guda 46, ciki har da buƙatar neman samar da Jihar Katagum daga cikin Jihar Bauchi. Sai dai, a rahoton da aka yada, babu sunan Katagum a cikin wadanda aka ce majalisar ta amince da su, lamarin da ya sanya jama’a da dama daga yankin suka fara ƙorafi da nuna matuƙar damuwa. 

Jihohin da aka ce an amince da su sun hada da a yankin Kudu Maso Yamma, Ijebu (daga cikin Jihar Ogun) da Ibadan (daga cikin Jihar Oyo), Kudu Maso Gabas, Anim (daga yankunan jihohin Anambra da Imo ) da kuma sabuwar Jihar Adada (daga cikin Jihar Inugu), Kudu Maso Kudu kuwa, Toru-Ibe (daga sassan Jihohin Ondo, Edo, da ɗelta) da kuma Obolo (daga Akwa Ibom), Arewa Maso Gabas, Saɓanna (daga Jihar Borno) da Amana (daga Jihar Adamawa), Arewa Maso Yamma, Tiga (daga cikin Jihar Kano) da Gurara (daga kudancin Jihar  Kaduna) da kuma yankin Arewa ta Tsakiya, Okura (daga Jihar Kogi State) da kuma Apa (daga cikin Jihar Benuwe).

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas

Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara

Sai dai tuni masu sanatoci da dama, kamar Sanata Shehu Buba, da Sanata Abdul Ahmad Ningi da ke wakiltar Bauchi ta tsakiya suka ƙaryata labarin da cewa babu gaskiya a cikinsa tare da neman jama’a da su yi watsi da shi.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas
Labarai

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas

October 2, 2025
Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara
Siyasa

Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara

September 28, 2025
Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas
Siyasa

Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas

September 27, 2025
Next Post
Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version