Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama tawagar mata ta ƙwallon kwando ta Nijeriya, D’Tigress, da lambar yabo ta ƙasa da kuma tukuicin dala $100,000 ga kowace ƴar wasa, saboda nasarar da suka samu a gasar cin kofin FIBA ta shekarar 2025.
Shugaban ƙasar ya kuma bai wa kowane memba na kwamitin horar da ƴan wasan kyautar dala $50,000, a wani mataki na nuna gamsuwa da gudunmawar da suka bayar wajen ganin Nijeriya ta samu nasarar lashe kofin karo na biyar a jere.
- Kashe N712bn Kan Gyaran Filin Jiragen Saman Legas Rashin Sanin Ya Kamata Ne – ADC
- Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da ya karɓi tawagar a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Ya yaba da jajircewa, da ɗa’a da ƙwarewa da ƴan wasan suka nuna, yana mai cewa su ne abin koyi ga matasa a fannin wasanni da kishin ƙasa.
D’Tigress ta doke Senegal a wasan ƙarshe na gasar, abin da ya tabbatar da matsayin Nijeriya a matsayin cibiyar ƙwallon kwando ta mata a nahiyar Afrika.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp