Uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta ba da tallafin Naira biliyan ɗaya da kayan agaji ga mutanen da ambaliya, hatsarin jirgin ruwa, hare-haren ‘yan bindiga da gobara suka shafa a Jihar Neja.
Tallafin ya haɗa da buhun shinkafa 2,000, atamfa 16,000 ga mata, kaya da takalma sama da guda 100.
- Kwamishinan Sufuri Ya Yi Murabus Kan Belin Wani Da Ake Zargi Da Laifin Safarar Kwaya A Kano
- Hare-haren Boko Haram Da ‘Yan Bindiga Ya Ragu A Cikin Shekaru Biyu – Ribadu
A ziyarar da ta kai jihar, ta ce wannan tallafi na cikin shirin ‘Renewed Hope Initiative’ domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa.
Ta kuma yi addu’a ga iyalan da suka rasa ‘yan uwa da waɗanda suka rasa matsuguni.
Gwamna Umaru Bago ya gode mata bisa wannan taimako, inda ya bayyana cewa ku6din an riga an tura su asusun tallafin gaggawa na jihar.
Ya kuma ce za a yi amfani da su wajen taimaka wa waɗanda abin ya shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp