Alummar duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan furucin firaministan Israila na fadada mamaya a Gaza.
Sakamakon wani nazarin jin raayin jamaa da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 86.6 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana adawa mai karfi da matakin firaministan, suna masu kira da Israila ta dakatar da bude wuta da kawo karshen rikici da Gaza nan take.
Sakamakon ya kuma nuna cewa, kaso 80.8 na wadanda suka amsa na ganin cewa mafita ga rikicin Palasdinu ya dogara ne da kafuwar kasashe biyu, inda suka yi kira da a dawo da halaltattun hakkokin kasar Palasdinu.
Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne a dandalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 9,093 suka bayar da amsa da bayyana raayoyinsu cikin saoi 24. (Faiza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp