ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, June 22, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu

by Shehu Yahaya
11 months ago
Jirgin

Gwamnatin tarayya ta kashe kimanin naira biliyan 26.38 wajen kula da jiragen saman shugaban ƙasa a cikin wata 18 na farkon mulkin Shugaba Bola Tinubu, wanda ke nunawa cewa ana ci gaba da kashe ma-ƙudan kuɗaɗe wajen kula da jiragen duk da kiraye-kirayen da ake yi wajen rage kashe kuɗaɗe.

Binciken bayanan kashe kuɗaɗen da aka samu daga Goɓspend, wani dandamali na fasahar kan bibiyar yadda gwamnati ke kashe kuɗaɗe, ya bayyana cewa an ƙaddamar da kashe kuɗaɗen ne a tsakanin Yulin 2023 da Disamba 2024 don kula da ayyuka da jigilar jiragen.

A halin yanzu dai, bincike ya nuna cewa tsakanin 2016 da 2022, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ware naira biliyan 81.80 don kula da jiragen sama na shugaban ƙasa da tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje. Wannan adadi ya haɗa da naira biliyan 62.47 don gudanar da aiki da kula da PAF da nai-ra biliyan 17.29 don tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje da na gida, da kuma naira biliyan 2.04 da aka tanadar don wasu ayyuka da suka shafi wannan.

ADVERTISEMENT

A lokacin, fadar shugaban ƙasa tana da jiragen sama da 10 tun daga farkon gwamnatin Buhari a watan Mayu 2015.

Wasu masana masana’antu na ganin cewa kashe maƙudan kuɗaɗen na ƙara raunata darajar naira, saboda dukkan harkokin sufurin sama ana gudanar da su ne da dala. Wasu kuma su ganin  cewa fadar shugaban ƙasa ba ta kyautawa, domin suna ganin cewa kuɗaɗen da ya kamata a yi wa al’umma ayyukan raya ƙasa da su amma ana ci gaba da kashe wa jiragen saman shugaban ƙasa.

LABARAI MASU NASABA

Yanzu-Yanzu: An Kashe Manoma 18 Da Raunata Wasu A Wani Sabon Hari A Filato

Yanzu-Yanzu: Firaiministan Birtaniya Keir Starmer Ya Yi Murabus

  • Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar
  • An Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 30 A Wani Harin Jirgin Sama A Wurin Daurin Aure A Zamfara

A cewar Goɓspend, an kashe maƙudan kuɗaɗe a ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu a tsakanin Afrilu da Agusta 2024 wajen kula da jiragen saman shugaban ƙasa.

Farkon kashe kuɗaɗen a ranar 14 ga Yulin 2023, lokacin da aka biya naira miliyan 846.03 a matsayin kuɗaɗen tafiye-tafiyen shugaban ƙasa na wucin gadi. Kwanaki biyu daga bisani, an sake kashe naira miliyan 674.82. A wannan watan kaɗai, jirgin ya laƙume sama da naira biliyan 1.5.

A watan Agusta, kashe kuɗaɗen sun ƙaru. An kashe naira biliyan 2 a ranar 16 ga Agusta, kuma an rubuta ƙarin kuɗaɗe na naira miliyan 387.6 da naira miliyan 713.22 a wannan watan. A cikin zangon ƙarshe na shekara ta 2023, an kashe naira biliyan 1.26 a watan Nuwamba.

Shekarar 2024 ma ta fara ne da ƙarin kashe kuɗaɗe masu yawa. A watan Maris kaɗai, an kashe kuɗaɗe har sau biyu na naira biliyan 1.27 kowanne a ranar 7 da 9 na wannan watan. Wannan ya biyo bayan nai-ra biliyan 5.08 a ranar 23 ga Afrilu, wanda shi ne mafi girma a cikin kashe kuɗaɗe a watanni 18 da aka gudanar da binciken.

A ranar 8 ga Mayu da 11 ga Mayu, an kashe naira biliyan 2.43 da naira biliyan 1.27 a jere, tare da wani ƙarin naira biliyan 1.27 da aka aike a ranar 25 ga Mayu. A ranar 5 ga Agusta, gwamnatin ta baya naira biliyan 1.25 da naira biliyan 2.21, sannan a ranar 6 ga Agusta, naira miliyan 902.9 da naira biliyan 1.24 aka kashe. Jimlar dukkanin abin da aka kashe a watan Agusta ya kai sama da naira biliyan 5.6.

Biyan kuɗin ya ci gaba har zuwa ƙarshen kwata na hudu na 2024, duk da haka a cikin ƙarancin adadi. Waɗanda sunka haɗa da naira miliyan 160.4, a ranar 8 ga Agusta, naira miliyan 35, a ranar 11 ga Sa-tumba, naira milian 133, a ranar 29 ga Satumba, da jerin biyan kuɗaɗe masu ƙaranci a Disamba, ciki har da na naira miliyan 290 da naira miliyan 102.95 da naira miliyan 25.25 da naira miliyan 8.7.

Jirgin saman shugaban ƙasa, wanda rundunar sojin saman Nijeriya ke kula da shi, ana amfani da shi ne wajen yin sufuri na sama na shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa da manyan jami’an gwamna-ti. Duk da cewa yana da matuƙar muhimmanci, amma kuɗaɗen da ake kashewa wajen kulawa da jirgin ya kasance batun da ake tattaunawa da sukan lamarin, musamman ma a cikin yanayin matsalolin kuɗi da Nijeriya kef ama da shi.

Jirgin
Shehu Yahaya
+ postsBio
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Matasa 1,200 Sun Amfana Da Horon Sana’o’i Ƙarƙashin Shirin ‘Renewed Hope’ A Kaduna
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Ranar Dimokuraɗiyya: Gwamna Uba Sani Ya ‘Yanta Fursunoni 97
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Gwamna Sani Ya Kashe Sama Da Naira Biliyan Ɗaya Kan Tallafin Ɗalibai A Kaduna – Kwamishina
  • Shehu Yahaya
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-yahaya/
    Uba Sani Ya Sanya Hannu Kan Sabbin Dokoki A Bangaren Sauya Fannin Wuta, Noma, Da Muhalli

MASU ALAKA

Yanzu-Yanzu: An Kashe Manoma 18 Da Raunata Wasu A Wani Sabon Hari A Filato
Manyan Labarai

Yanzu-Yanzu: An Kashe Manoma 18 Da Raunata Wasu A Wani Sabon Hari A Filato

June 22, 2026
Yanzu-Yanzu: Firaiministan Birtaniya Keir Starmer Ya Yi Murabus
Labarai

Yanzu-Yanzu: Firaiministan Birtaniya Keir Starmer Ya Yi Murabus

June 22, 2026
Sojoji Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace, Sun Daƙile Hari A Kaduna Da Zamfara
Manyan Labarai

Sojoji Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace, Sun Daƙile Hari A Kaduna Da Zamfara

June 22, 2026
Next Post
Ziyarar Manzon Allah (SAW) A Madinah (1)

Fisatattun Matasa Sun Ƙone Wata Mata Ƙurmus Kan Jita-Jitar Satar Yara A Kaduna

Fisatattun Matasa Sun Ƙone Wata Mata Ƙurmus Kan Jita-Jitar Satar Yara A Kaduna

June 22, 2026

Mutane 842 Ne Suka Rasa Ransu, Aka Yi Garkuwa Da Sama Da 270 A Watan Mayu – Rahoto

June 21, 2026
PRP Ta Zargi Kwankwaso Da Saye Fom Ɗin Takarar  Jamiyyar

PRP Ta Zargi Kwankwaso Da Saye Fom Ɗin Takarar Jamiyyar

June 21, 2026
An Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Daji 2,187 A Bauchi

An Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Daji 2,187 A Bauchi

June 21, 2026
An Sanar Da Wadanda Suka Lashe Golden Goblet Na Bikin Fina-Finen Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

An Sanar Da Wadanda Suka Lashe Golden Goblet Na Bikin Fina-Finen Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

June 21, 2026
Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi

Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi

June 21, 2026
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 21, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.