A kowace shekara, Nijeriya na tafka asarar dala biliyan biyu, kwatankwacin Naira tiriliyan 3.2, sakamakon watsi da yin nona a Gandun Dazukan ƙasar.
Wasu ƙwararru a fannin aikin noma ne suka bayyana hakan, inda suka sanar da cewa; idan da ana gudanar da ayyukan noma a Gandun Dazukan ƙasar, za a iya ƙara bunƙasa tattalin arziƙin kasuwanci na ƙasar.
Kazalika, sun yi nuni da cewa; idan da ana amfani da Gandun Dazukan wajen yin noma, da za a iya ƙara faɗaɗa harkar kusuwancin noma.
Har ila yau, sun ƙara da cewa; hakan kuma zai sanya a ƙara samar da ayyukan yi a tsakanin mata da matasa, ta yadda ƙananan manona da ƙananan masu sarrafa amfanin gona a ƙasar za su ɗauke su, su riƙa yi musu aiki.
Shugaban ƙungiyar manoma don samun riba na ƙasa, Ibrahim Kabiru ya bayyana cewa; ta hanyar yin shuke-shuken kamar kayan marmari da suka haɗa da bishiyoyin Mangoro, Lemon zaƙi, Gwaiba, Kwakwar Manja da sauran makamantansu a Gandun Dazukan ƙasar, Nijeriya za ta iya samun kuɗaɗen shiga da yawansu ya kai kimanin dala biliyan biyu, daidai da Naira tiriliyan 3.2.
- Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana
- Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Zama Sakatariyar Kungiyar Yaƙi Da Cutar Daji
“Ta hanyar gudanar da ɗimbin ayyukan noma a Gandun Dazukan wannan ƙasa, zai yi matuƙar ƙara yawan ayyukan masana’antun ƙasar da ke sarrafa amfanin gona domin fitarwa zuwa kasuwannin duniya, don sayarwa”, in ji Ibrahim.
Kazalika, Ibrahim wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar manoma ta ƙasa (AFAN) ya jaddada cewa; idan aka samu goyon bayan ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci da kuma goyon bayan sauran hukumomin, hakan zai bayar da damar gyara Gandun Dazukan da ake da su, musamman wajen kare su daga kwararowar hamada.
Shugaban ya ƙara da cewa, akasarin noman gargajiya a ƙasar nan, ana yin sa ne a karkara, inda manoma a karkara ke shuka ‘ya’yan itatuwa na kayan marmari a Gandun Dazukan ƙasar.
Ya ci gaba da cewa, mazauna karkara na yin amfani da Gandun Dazukan ƙasar wajen yin kiwon dabbobi, wanda hakan ke ƙara bunƙasa ayyuka a tsakanin mazauna karkarar.
Shugaban ya yi nuni da cewa, gudanar da ayyukan noma a Gandun Dazukan wannan ƙasa, zai yi matuƙar kawo ci gaba ga Nijeriya tare da samar da ɗauki ga marasa ƙarfi, wanda kuma hakan zai bai wa mata da matasa damar jawo su a jiki, domin tafiya tare da su.
A cewarsa, har yanzu ba a makara ba, domin kuwa za a iya yin amfani da Gandun Dazukan ƙasar wajen gudanar da ayyukan noma.
Shugaban ya ci gaba da cewa, hakan zai ƙara taimaka wa a samar da wadataccen abinci a ƙasar da kare kwararowar hamada da kuma annobar sauyin yanayi.
Ya bayyana cewa, za a iya cimma hakan ne kaɗai idan mahukunta a ƙasar suka samar da kyakywan tsari tare da gangamin wayar da kan jama’a da kuma zuba hannun jari
a fannin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp