Jakadan kasar Sin da ke Najeriya, Yu Dunhai, ya gana a kwanan nan da ministar kula da harkokin masana’antu, da cinikayya, da zuba jari ta tarayyar Najeriya, madam Jumoke Oduwole.
Jakada Yu ya bayyana cewa, tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci kasar Sin tare da halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a watan Satumban bara, zuwa yanzu, Sin da Najeriya na kara samun fahimtar juna ta fuskar siyasa, tare da fadada hadin-gwiwa a bangarorin da suka shafi masana’antu, cinikayya da zuba jari, har ma kwalliya ta biya kudin sabulu. Ya ce kasar Sin tana fatan ita da Najeriya za su rattaba hannu kan yarjejeniyar raya dangantakar abokantaka a fannin tattalin arziki, don aiwatar da matakin soke haraji da kashi 100 bisa 100 a kan kayayyakin Najeriya, a wani kokari na taimaka wa Najeriya kara fitar da kayayyakinta zuwa kasar Sin, da daukaka ci gaban dangantakar kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni, gami da raya al’ummomin kasashen biyu masu kyakkyawar makoma ta bai daya.
A nata bangaren, madam Jumoke Oduwole ta ce, matakin kasar Sin na soke buga haraji da kashi 100 bisa 100 a kan kayayyakin kasashen Afirka da suka kulla dangantakar jakadanci da ita, ya samu karbuwa sosai daga sassan kasa da kasa, inda Najeriya take matukar yabawa da cikakken goyon-bayan kasar Sin gare ta a fannin raya zaman rayuwar al’umma da tattalin arziki. Haka kuma, Najeriya tana fatan kara tuntubar kasar Sin, da aiwatar da manufofi a zahiri, ta yadda matakin na soke haraji zai amfani al’ummar Najeriya. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp