Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Charles Soludo, ya bayyana cewa ba shi da wata nadama kan goyon bayan da ya nuna a fili ga Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, duk da kasancewarsa a jam’iyyar adawa.
Soludo ya bayyana haka a ranar Talata yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa bayan wata ganawa da Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
- Gwamnatin Kano Za Ta Horar Da Tubabbun ‘Yandaba 718 Sana’o’i
- ’Yan Bindiga Sun Sace Fasinjoji 6 A Taraba
Ya bayyana ganawar a matsayin mai ciki da daɗi, ya kuma ya yaba da yanayin lafiyar Shugaba Tinubu. “Shugaban Ƙasa yana cikin ƙoshin lafiya da kuzari, kuma na ji daɗin ganawa da shi. Lallai ganawa ce mai matuƙar daɗi da farinciki,” in ji Soludo.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya fito ƙarara ya goyi bayan shugaban ƙasa wanda ba a cikin jam’iyyarsu yake, Soludo ya ce goyon bayansa ga Tinubu ba sabon abu ba ne.
“An samar da waɗannan huluna tun lokacin da Shugaban Ƙasa ya ziyarci Jihar Anambra kuma kun ga allunan talla da sauran abubuwa da ke bayyana cewa masu ra’ayin kowa ci gaba suna aiki tare ne da juna,” in ji Soludo.
“Bayan haka, wannan wata babbar manufa ce da na yi imani da ita sosai, cewa ya kamata dukkan jam’iyyun siyasa da ke ikirarin ra’ayin ci gaba su haɗu a ƙarƙashin wata babbar ƙawance don zurfafa tunani da kawo ci gaba ba kawai a tafarkin dimokuradiyyarmu ba, har ma da ci gaban tattalin arziki da zamantakewar kasarmu.”
Gwamnan ya jaddada cewa kiransa na ganin masu ra’ayin ci gaba sun yi aiki tare ya samo asali ne daga yaƙini da kuma daɗaɗɗiyar alaƙar da ke tsakaninsa da Shugaban Ƙasa.
“Idan na ce masu ra’ayin ci gaba su yi aiki tare, kira ne ga duk masu magana kan Shugaba Bola Ahmed Tinubu… Ina nufin, ba ni da wani uzuri game da hakan.
“Shugaba Tinubu abokina ne, abokina ne tun shekaru 22 da suka gabata zuwa yanzu.
“Abokina ne, ina goyon bayansa, kuma na gamsu da matakan da ya ɗauka, musamman a fannin tattalin arziki, kuma na bayyana hakan ba sau ɗaya ba, muna kan hanyar ƙwarai kuma muna buƙatar mu ci gaba a haka,” in ji Soludo.
Game da halin tsaro a Jihar Anambra, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta ɗauki wani tsari na bai-daya tun daga watan Janairu, biyo bayan zartar da dokar tsaron cikin gida a jihar.
“Ana kokarin tunkarar matsalar rashin tsaro ne tun daga tushe. Dukkanin miyagun ‘yan ta’adda sun tsere daga jihar saboda su ne ke yaudarar matasanmu da kuma jefa su cikin aikata laifuka,” in ji shi.
Soludo ya ce gwamnati na amfani da matakan karfi da na lallashi don magance matsalar rashin tsaro.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp