Ƙaramar Hukumar Safana a Jihar Katsina ta amince ta yi sulhu da ‘yan bindiga domin kawo ƙarshen hare-hare da tashin hankali a yankin.
Kafin Safana, ƙananan hukumomin Jibiya, Batsari da Dan Musa sun riga sun yi irin wannan yarjejeniya, wacce ta taimaka wajen rage hare-hare, dawo da tsaro, da bai wa manoma da ‘yan kasuwa damar komawa harkokinsu cikin kwanciyar hankali.
- Allah Zai Kunyata Masu Ɗaukar Nauyin ’Yan Ta’adda – Gwamnan Zamfara
- Rangwame: Tinubu Ya Bada Umarnin Sake Bitar Tsarin Yadda Ake Karɓar Haraji
A yarjejeniyar, ‘yan bindiga sun yadda za su daina kai hare-hare a Safana, su sako duk wanda suke tsare, yayin da gwamnati za ta gyara musu madatsun ruwa da dam-dam don shayar da dabbobinsu, tare da gyara asibitoci, makarantu domin koyar da ‘ya’yansu.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Safana, Abdullahi Sani Safana, ya ce ‘yan bindigan da kansu suka nemi a yi sulhu bayan ganin irin nasarar da aka samu a wasu ƙananan hukumomi.
Ya ƙara da cewa ‘yan bindigan sun buƙaci ƙananan hukumomin Kurfi da Dutsinma su yi irin wannan yarjejeniyar.
Wani mazaunin Safana, Iliyasu Sani, ya ce sulhun ya kawo sauƙi ga rayuwar jama’a, domin yanzu suna iya zuwa kasuwa da yin noma ba tare da fargaba ba.
Masani a fannin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce talauci da rashin tsaro ne suka sa jama’a neman mafita da kansu.
Ya kuma bayyana cewa idan duk ɓangarorin suka tsaya kan alƙawarin da aka yi, wannan sulhu na iya zama mataki na farko na samun zaman lafiya na dindindin a yankin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp