Kwamandan runduna ta daya ta sojin Nijeriya, Janar Taoreed Lagbaja, ya yi nasarar ceto wasu mutane da ‘yan bindiga suka yi garkuwa dasu a karamar hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna.
Daraktan Yada Labaran Rundunar Sojin Nijeriya, Birgediya Janar Onyeama Nwachukwu, ya ce tawagar kwamandan ta ci karo da masu garkuwa da mutanen ne a kauyen Manini da ke kan hanyar zuwa Birnin Gwari, lokacin da suke ziyarar duba sojojin da suke aiki a yankin.
- Yadda ‘Yan Kasuwar Kwari Ke Tafka Asara Saboda Ambaliyar Ruwa A Kano
- Mutane 2 Sun Mutu, An Ceto 5 Yayin Da Gini Ya Rufta A Abuja
Sanarwar ta ce yayin musayar wuta, ‘yan bindigar da suka samu raunuka, sun tsere zuwa cikin daji, inda suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.
Nwachukwu ya bayyana wadanda aka ceton a matsayin maza biyu da mace guda, inda ya ce yanzu haka ana duba lafiyarsu a asibitin Kaduna.
Hanyar Birnin Gwari a Jihar Kaduna ta zama tarkon mutuwa, inda a kusan kullum mahara ke kashe tare da sace matafiya da kuma daidaikun mutane.