• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gidauniya Ta Rabar Da Buhun Takin Zamani 6,000 Ga Manoma A Bauchi 

by Khalid Idris Doya and Sulaiman
2 months ago
Taki

Gidauniyar Wunti Al-Khair ta ƙaddamar da rabon takin zamani buhu 6,000 kyauta ga manoma a faɗin jihar Bauchi domin bunƙasa harkokin noma da wadata jihar da kayan abinci. 

 

Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamar da rabon a ranar Alhamis, Abubakar Mohammed ‘Yanmaza, jami’in sa ido na gidauniyar, ya ce wannan rabon shi ne karo na huɗu da gidauniyar ke raba wa manoma kyautar takin zamani domin agaza musu a fannin noma.

  • An Samu Gagarumin Ci Gaba Kan Habaka Fasahar Zamani Ta Sin Yayin Shirin Raya Kasa Na Shekaru Biyar Na 14 
  • ‘Yansanda Sun Kama Wani Mai Garkuwa Da Mutane, Sun Ceto Wani Yaro Ɗan shekara 2 A Yobe

Ya ce rabon na cikin manufar gidauniyar na taimaka wa manoma ne musamman masu ƙaramin karfi domin bunkasa harkokin noma a jihar.

 

LABARAI MASU NASABA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

“Kowa ya sani wadatar abinci yana ɗaya daga cikin alamun da ke nuna kyautatawar tattalin arziki na ƙasa baki ɗaya, don haka ne muka himmatu wajen ba da namu gudunmawar ta wannan fannin.”

 

Ya kara da cewa, an kafa gidauniyar ne domin taimakawa a ɓangaren kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki wanda rabon takin na daga cikin shirin gidauniyar na bunƙasa tattalin arziki, da kuma kyautata ci gaban al’umma.

 

“Wannan shi ne karo na huɗu da wannan gidauniyar ta ke rabon taki duk shekara ga manoma masu ƙaramin ƙarfi da ba za su iya sayen takin a irin wannan lokacin da gona ke buƙata ba.”

 

“An ware buhun taki guda 6,000 da za a rabar wa manoma masu ƙaramin karfi a dukkanin faɗin jihar Bauchi,” in ji shi.

 

‘Yanmaza ya nuna cewa an yi tsari na musamman domin tabbatar da asalin waɗanda aka zaɓo ne za su amfana da takin, ya yi gargaɗi kan cewa duk wanda aka kama da kauce wa asalin tsarin da aka samar da takin domin su zai ɗanɗana kuɗarsa.

 

Shi ma da ya ke ƙarin haske, jami’i a gidauniyar, Isyaka Isma’i Wunti, ya ce bayan ƙaddamar da rabon a cikin garin Bauchi za a zaga sauran shiyyoyin Bauchi da sauran yankuna domin yin rabon domin tabbatar da takin ya shigo hannun manoma a lungu da sako a na jihar.

 

Ya yi gargaɗin cewa kada waɗanda aka raba musu takin su je su sayar, ya nemi su tabbatar sun yi amfani da su ta hanyoyin da suka dace domin bunƙasa harkokin abinci da wata jihar da kayan abinci.

 

Ya kuma ce an yi adalci sosai wajen zaɓo masu cin gajiyar shirin a kowani lungu da sako. Inda ya ce an yi tsarin sosai na yadda asalin manoma kuma masu ƙaramin karfi ne za su amfana da tallafin.

 

Emmanuel Samson, daga cikin masu cin gajiyar tallafin, ya gode wa wanda ya assasa gidauniyar, Alhaji Bala Maija’ama Wunti bisa wannan tallafin, ya ce tallafin zai taimaka musu matuƙa wajen amfanin gona.

 

Salisu Muhammad Maidawa, ya ce, “Ba abin da za mu ce sai godiya ga wanda ya assasa wannan gidauniyar, yadda yake faranta wa jama’a rai ta fuskokin rayuwa daban-daban muna roƙon Allah ya faranta masa rai, abun da ya ke nema na alkairi Allah ya cika masa.”

 

“A zahirin gaskiya wannan tallafin ya zo a kan gaɓa domin kamar muna tsananin halin buƙatar takin zamani sai kuma ga shi Allah ya sa zan samu kyautarsa.”

 

Da yawan waɗanda suka ci gajiyar sun sha alwashin amfani da takin ta hanyoyin da su dace ba tare da sayarwa ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi
Labarai

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza
Labarai

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar
Labarai

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Next Post
Tsarin Samar Da Kayayyaki Na Masana’antar Lantarki Ya Ci Gaba Da Samun Karfin Juriya A Kasar Sin

Tsarin Samar Da Kayayyaki Na Masana’antar Lantarki Ya Ci Gaba Da Samun Karfin Juriya A Kasar Sin

LABARAI MASU NASABA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

October 19, 2025
Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.