A yau Juma’a ne kasar Japan ta gudanar da gangamin tunawa da wadanda suka rasa rayukansu yayin yakin duniya na biyu, sai dai yayin da yake jawabi albarkacin taron, firaministan kasar Shigeru Ishiba, bai tabo batu kan alhakin dake rataye a wuyan kasarsa ba, a matsayinta na wadda ta mamayi wasu kasashen nahiyar Asiya. A hannu guda kuma ya gabatar da addu’a ga wurin ibadar nan na Yasukuni, a matsayin girmmawa ga wurin ibadar da ake kallo a matsayin wurin da aka karrama mutanen da suka tafka danyen aiki yayin yakin duniya na biyu. Kazalika, wasu ministocin kasar sun kaiwa wurin ibadar na Yasukuni ziyarar girmamawa.
Jerin wadannan matakai dai na shan suka, da adawa daga sassan kasa da kasa. Inda wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar game da hakan ta nuna cewa, kaso 64.4 bisa dari na masu bayyana ra’ayin na adawa da ziyarar ‘yan siyasar na Japan zuwa wurin ibadar. Kana kaso 55.3 bisa dari sun soki lamirin Japan bisa yadda ta kawar da kai daga abun da ya auku na tarihin wurin. Kazalika, kaso 65.2 bisa dari sun soki matakin Japan na sauya bayanai dake kunshe cikin litattafan tarihi masu nasaba da batun. Sai kuma kaso 65.7 bisa dari da suka yi kira ga gwamnatin Japan da ta nemi afuwar kasashen da mamayarta ta cutar tare da biyansu diyya.
Wannan dai batu ya haifar da bayyana matukar rashin jin dadi tsakanin al’ummun nahiyar Asiya, ciki har da al’ummun Koriya ta Kudu, da sukarsu game da hakan ya haura kaso 90 bisa dari. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp