Wani kwararen Malamin Gona da aiki a karkashin shirin bunkasa aikin Gona na jihar Baluchi BSAD, Lawan Nura, ya koka kan yadda ake ake sayar da wasu kayan aikin gona da ba riga an tantance su ba a kasuwanin da ke a fadin kasar nan.
Ya yi gargadi da cewa, wannan dabi’ar, za ta iya jefa rayuwar manoma da masu yin amfani da amfanin gona da aka noma da kuma shafar muhalli.
- Hukumar NABDA Ta Bukaci Musulmi Su Cire Fargabar Amfani Da Fasahar Alkinta Halittu
- Ya Kamata A Yi Wa Japan Jinyar Cutar “Mantuwar Tarihi”
Nura wanda ya bayyana hakan a wata hira da aka yi dashi, ya nuna damuwarsa, kan yadda ake saba ka’idojin da suka da ce, na gabatar da kayan aikin gona, a kasuwanin, kamar irinsu, takin zamani da magungunan feshi da sauransu.
Ya kara da cewa, malaman aikin gona wadanda suka kasance sune kwararru suka kuma samu isashen haro a fannin aikin noma, mussaman wadanda kuma subane laka da cibiyoyin kula da binciken aikin noma, amma irin wadannan masu sarrafa kayan aikin gonar, sai su ki tuntubar mu.
Nura ya buga misali da Buhun Takin zamani na Di-ammonium Phosphate wanda a jikin Buhun aka rubuta karara cewa, ba na ssyarwa bane, kuma ba domin amfanin bukatda zalika,aka yi ba, amma kuma sai a ganshi, ana sayar da shi karara, kasuwanin kasar nan.
Ya yi gargadi da cewa, wadannan gundarin kayan aikin gonar ba wai ana yin amfani da su kai tsaye a gonai ba ne, inda ya kara da cewa yin amfani da su, zai iya rage yawan amfanin gona da manomi ya kamata ya samu tare da kuma shafar lafiyar,mutanen da suka yi amfani da su.
Kazalika, ya yi kira ga gwamnati da ta dawo da ta kara tsaurara matakan bin ka’idojin sarrafa kayan aikin gona kafin fitar da su zuwa kasuwanni domin sayarwa da manoma.
Ya shawarci manoma da su tabbatar da suna tuntubar malaman gona kafin yin amfani da duk wasu kayan aikin gona da ba su da masaniya akansu.
“ Mu malaman gona a shirye muke ako da yaushe domin mu taimaka wa manoma kuma akwai bukatar mu yi aiki kafada da kafada domin tabbatar da samar da kariya ga amfanin gona da kuke nomawa”Inji Nura..
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp