• English
  • Business News
Thursday, August 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Rashin Zuwa Majalisa Ne Yasa Kamfani Auyo Ba Ya Ɗaukar Nauyin Ƙuduri – Inji Agbese

by Abubakar Sulaiman
5 days ago
in Siyasa
0
Rashin Zuwa Majalisa Ne Yasa Kamfani Auyo Ba Ya Ɗaukar Nauyin Ƙuduri – Inji Agbese
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Philip Agbese, ya ƙaryata zargin da ɗan majalisar Jigawa, Hon. Ibrahim Auyo, ya yi cewa ana biyan miliyoyi kafin a gabatar da ƙudurori. Ya ce wannan magana “ba haka ba ne” kuma wani yunƙuri ne na ɓoye rashin aikin wakilin daga idon jama’a.

Agbese ya bayyana cewa Auyo na fama da matsalar rashin lafiya da suka hana shi halartar zaman majalisa yadda ya kamata ba, inda a cewarsa bai kai kashi 10 cikin 100 na halarta ba tun daga 2023, kuma bai taɓa gabatar da ko kudurori, ko doka ko ƙorafin mutanensa  ba.

  • Majalisar Kano Ta Dakatar Da Shugaban Karamar Hukuma Bisa Zargin Kara Farashin Takin Gwamnati
  • Jigawa Ta Fitar Da ₦1.5bn Na Lamunin Noma Ga Ma’aikatan Gwamnati Kashi Na Biyu

Ya ce ba daidai ba ne ya rika ƙirƙirar labaran ƙarya don ɓoye rashin aikinsa ba, inda ya ƙara da cewa majalisar ƙarƙashin jagorancin Kakakinta Tajudeen Abbas na tafiya ne bisa gaskiya ba tare da karɓar cin hanci ba.

Agbese ya shawarci Auyo da ya mayar da hankali kan lafiyarsa da wakilcin mazaɓarsa maimakon ya ɓata sunan majalisar, yana mai ƙara wa da cewa idan akwai wata shaida ta rashin gaskiya ya gabatar da ita gaban kwamitin ɗa’a da hukunce-hukuncen majalisa.

Har zuwa lokacin kammala wannan rahoto dai, ba a samu martanin ɗan Majalisa Kamfani Auyo ba yayin da wayarsa ta kasance a kashe.

Labarai Masu Nasaba

Daga Sawaba Zuwa Asara: Baje Kolin Kasuwancin Siyasa A Kano – Auwalu Anwar

Tinubu Ya Ci Amanar Kano, Babu Batun Haɗin Guiwa Tsakaninsa Da Kwankwaso A 2027 – Galadima

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: APCAuyo
ShareTweetSendShare
Previous Post

Zaɓen Cike Gurbi: DSS Ta Kama Wani Jam’in Jam’iyya Da Maƙudan Kuɗaɗe A Kaduna

Next Post

Kungiyoyi Masu Fada Aji Kan Harkar Ilimi Sun Nemi A Yi Wa Sashen Kwaskwarima

Related

Hoton Kwankwaso da Ganduje da Shekarau
Bakon Marubuci

Daga Sawaba Zuwa Asara: Baje Kolin Kasuwancin Siyasa A Kano – Auwalu Anwar

1 day ago
Na Yafe Wa Buhari Duk Abin Da Ya Min – Buba Galadima
Manyan Labarai

Tinubu Ya Ci Amanar Kano, Babu Batun Haɗin Guiwa Tsakaninsa Da Kwankwaso A 2027 – Galadima

2 days ago
Idan Jonathan Ya Tsaya Takara A 2027, Girmansa Zai Faɗi – Shehu Sani
Manyan Labarai

Idan Jonathan Ya Tsaya Takara A 2027, Girmansa Zai Faɗi – Shehu Sani

2 days ago
PDP Ta Yi Fatali Da Sakamakon Zaɓen Cike Gurbi Na Okura, Ta Nemi A Soke
Siyasa

PDP Ta Yi Fatali Da Sakamakon Zaɓen Cike Gurbi Na Okura, Ta Nemi A Soke

3 days ago
PDP Ta Ƙalubalanci Sakamakon Zaɓen Cike Gurbi Na Garki/Babura A Jigawa
Siyasa

PDP Ta Ƙalubalanci Sakamakon Zaɓen Cike Gurbi Na Garki/Babura A Jigawa

4 days ago
APC Ta Lashe Zaɓen Cike Gurbi Na Garki/Babura A Jigawa
Labarai

APC Ta Lashe Zaɓen Cike Gurbi Na Garki/Babura A Jigawa

4 days ago
Next Post
Kungiyoyi Masu Fada Aji Kan Harkar Ilimi Sun Nemi A Yi Wa Sashen Kwaskwarima

Kungiyoyi Masu Fada Aji Kan Harkar Ilimi Sun Nemi A Yi Wa Sashen Kwaskwarima

LABARAI MASU NASABA

Mafi Ƙarancin Albashin ₦70,000 Ba Zai Iya Tsamo ‘Yan Nijeriya Daga Ƙangin Talauci Ba – Amurka

Mafi Ƙarancin Albashin ₦70,000 Ba Zai Iya Tsamo ‘Yan Nijeriya Daga Ƙangin Talauci Ba – Amurka

August 21, 2025
Sarkin Musulmi Ya Taya Ladoja Murnar Zama Sabon Sarkin Ƙasar Ibadan 

Sarkin Musulmi Ya Taya Ladoja Murnar Zama Sabon Sarkin Ƙasar Ibadan 

August 21, 2025
Boniface

Ac Milan Na Tattaunawa Da Bayern Leverkusen Akan Yunkurin Daukar Boniface

August 20, 2025
Xi Jinping Zai Duba Faretin Sojoji Ta Kan Titin Chang’an A Ranar Uku Ga Watan Satumba Dake Tafe

Xi Jinping Zai Duba Faretin Sojoji Ta Kan Titin Chang’an A Ranar Uku Ga Watan Satumba Dake Tafe

August 20, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Cibiyoyin Bayar Da Lamuni Kan Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci Cibiyoyin Bayar Da Lamuni Kan Tabbatar Da Gaskiya Da Adalci

August 20, 2025
Faretin Sojoji Da Sin Za Ta Gudanar Zai Shaida Muhimmancin Zaman Lafiya Da Goyon Bayan Gaskiya Da Adalci Tsakanin Kasa Da Kasa

Faretin Sojoji Da Sin Za Ta Gudanar Zai Shaida Muhimmancin Zaman Lafiya Da Goyon Bayan Gaskiya Da Adalci Tsakanin Kasa Da Kasa

August 20, 2025
Kasar Sin Za Ta Gabatar Da Sabbin Makamai Yayin Faretin Soja Na Ranar 3 Ga Watan Satumba

Kasar Sin Za Ta Gabatar Da Sabbin Makamai Yayin Faretin Soja Na Ranar 3 Ga Watan Satumba

August 20, 2025
Rajistar Katin Zaɓe: Gwamnatin Kano Za Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kan Jama’a 

Rajistar Katin Zaɓe: Gwamnatin Kano Za Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kan Jama’a 

August 20, 2025
Xizang A Shekaru 60 Da Kafuwa: Daga Mawuyacin Hali Zuwa Farin Wata Sha Kallo

Xizang A Shekaru 60 Da Kafuwa: Daga Mawuyacin Hali Zuwa Farin Wata Sha Kallo

August 20, 2025
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Hukumar ‘Yansanda Ta Yi Watsi Ga Ƙarin Girma Ga ASP 179, Ta Ɗaga Darajar 952 Zuwa DSP

August 20, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.