Dan Adam halitta ce mai saurin mantuwa. Duk da haka, akwai wasu abubuwa da ya kamata a tuna da su.
Abokai, ko kun san cewa, sama da shekaru 80 da suka gabata, ‘yan Najeriya da Sinawa sun taba yaki da sojojin Japan a Burma, inda suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen cin nasarar yakin da aka yi da ‘yan mulkin danniya, wato ‘yan Fascist a duniya?
- APC Ta Nemi A Soke Zaɓen Cike Gurbi A Kano Saboda Rikici
- Kungiyoyi Masu Fada Aji Kan Harkar Ilimi Sun Nemi A Yi Wa Sashen Kwaskwarima
A farkon shekarar 1944, Birtaniya ta tura wasu sojoji da aka dauka daga Najeriya, da Gold Coast (Ghana a yanzu) da sauran wurare, zuwa yankin kan iyakar Indiya da Burma. Daga lokacin har zuwa shekarar 1945, sojoji ‘yan Afirka sun yi ta kokarin yaki da sojojin Japan a Burma. Inda bajintar da wadannan sojojin Afirka suka nuna a yaki ta bar ma makiya mamaki matuka.
A lokacin kasar Sin ba ta tsaya kan tinkarar mahara Japanawa a ciki gidanta kadai ba, har ma bisa bukatar Birtaniyya, ta tura sojoji zuwa kasar Burma don tallafawa yakin da ake yi da sojojin Japan a can. Daga watan Oktoba na 1943 zuwa na Maris na 1945, sojojin kasar Sin sun hallaka sojojin Japan sama da 49,000, tare da kwato garuruwa da Japanawa suka mamaye sama da 50 a arewacin Burma. Sojojin kasar Sin sun kuma yi asara sosai, inda yawan mutanensu da suka rasa rai ko kuma suka ji rauni ya kai sama da 60,000.
Gudunmawar da magabata suka bayar, abu ne da ya kamata a tuna da shi. Mun san daga baya, tsoffin sojojin Afirka a yakin duniya na biyu sun taka muhimmiyar rawa a gwagwarmayar neman ‘yancin kai na kasashen Afirka, yayin da Sin ma ta tabbatar da matsayinta a idanun mutanen duniya, ta hanyar bayar da gagarumar gudummawa wajen yaki da ‘yan Fascist a duniya.
Kuma domin tunawa da tarihi ne, a jiya (15 ga watan Agusta, wato ranar cikar shekaru 80 da kasar Japan ta mika wuya ba tare da wani sharadi ba ga kawancen yaki da ‘yan Fascist), na ziyarci gidan tarihi na tunawa da yakin kin harin Japan da jama’ar kasar Sin suka yi, da ke birnin Beijing na Sin, domin maimaita tarihin yadda jama’ar kasar Sin suka yi tsayin daka wajen adawa da zaluncin mahara Japanawa. Ta hanyar kallon abubuwan da aka adana, da hotuna, da bidiyo, da rubutaccen bayanin da aka nuna, na sake gane wa idona irin ta’asar da mahara Japanawa suka aikata: kisan kiyashin da aka yi wa mutane kimanin 300,000 a Nanjing, babban birnin kasar Sin a lokacin; da yadda rundunar 731 ta kasar Japan ta gudanar da gwaje-gwajen kai tsaye kan jama’ar kasar Sin masu rai, don bincike da kera makaman kare dangi masu guba; da yadda sojojin Japan suka yi kokarin tabbatar da ganin a kona dukkan gidaje, da kashe dukkan mutane, da kuma kwace dukkan dukiyoyi, a dimbin kauyuka marasa adadi na kasar Sin. A sa’i daya kuma, na ji irin ruhin da jama’ar kasar Sin suke da shi na hakuri da jure wahalhalu, da yadda suke matukar kokari wajen tabbatar da samun nasara a yakin kin harin Japan. A yakin da aka kwashe shekaru 14 ana yinsa, kasar Sin ta samu asarar sojoji da fararen hula (mutuwa ko jin rauni) sama da miliyan 35, wato adadin kusan kashi daya bisa uku na jimillar wadanda suka mutu ko suka ji rauni a yakin duniya na biyu a fadin duniya.
Har ila yau, a zamanin da muke ciki, tunawa da tarihi yana da ma’anar musamman:
Ta hanyar tunawa da tarihi, muna dakile yunkurin mutanen da suke kokarin boye gaskiya, inda za mu tunatar da su cewa kisan kiyashi na Nanjing, da ta’asar da rundunar 731 ta aikata, abubuwa ne na gaske da suka taba faruwa, wadanda ba za a iya goge su daga cikin tarihi ba, kuma kasar Japan ba za ta iya tserewa alhakin laifukan cin zarafin bil’adama ba; kana za mu bayyana karara cewa, komawar yankin Taiwan zuwa cikin harabar kasar Sin yana daga cikin sakamakon da aka samu a yakin kin ‘yan Fascist a duniya, wadda ba za a iya gyara ta ba.
Haka zalika, tunawa da tarihi yana ba mu damar gadon ruhin hadin kai da gwagwarmaya. Jama’a daga ko’ina cikin duniya, ciki har da Afirka da Sin, sun taba yin hadin gwiwa karkashin tutar adalci, inda suka yi fafutuka kafada da kafada, don tabbatar da makoma mai haske ta bil’adama. Wannan ruhin yanzu an mai da shi ya zama niyyar gina “al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makomar bai daya,” wadda ta sanya mu yin aiki tare don samun zaman lafiya a duniya, da ci gaban bai daya a tsakanin dukkanin kasashe.
Tunawa da tabbatar da tarihi za su karfafa imaninmu kan cewar, wadanda ke neman yin kashin dankali a duniya ba za su samu biyan bukata ba, kuma nasara ta karshe za ta kasance ta mutane, da kasashe masu ra’ayin daukaka zaman lafiya da tabbatar da yanayin adalci a duniya. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp