Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya ce Sin ta bukaci Japan da ta yi karatun ta nutsu, ta waiwayi baya dangane da batutuwan danniya da ta aikata a tarihi, da al’amura irinsu batun wurin bautan nan na Yasukuni, kana ta sauya turba daga salon nuna karfin tuwo na soji, ta rungumi hanyar neman ci gaba ta turbar zaman lafiya, da neman amincewar makwaftanta na nahiyar Asiya, da sauran sassan kasa da kasa ta hanyar aiwatar da matakai na hakika.
Kakakin ya yi tsokacin ne yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, lokacin da aka nemi ya yi tsokaci game da matakin ‘yan siyasar Japan, na kai ziyara wurin bautan nan na Yasukuni, wurin ibadar da ake kallo a matsayin na karrama mutanen da suka tafka danyen aiki, yayin yakin duniya na biyu. (Saminu Alhassan)














